Rikici ya ɓarke a Siriya bayan tsagaita buɗe wuta
April 13, 2012Rahotanni daga ƙasar Siriya na cewar an samu wata taho mu gama tsakanin masu zanga-zanga da dakarun gwamnati a yankunan da ke kan iyakar ƙasar ta Syria da Turkiyya.
Rikicin dai ya ɓarke ne sanadiyyar harbin da dakarun gwamnati su ka yi na kan mai uwa da wabi yayin da wasu mutane su ka gudanar da zanga-zanga a dandalin Assi, wanda hakan ya yi sanadiyyar rasuwar mutum guda.
Baya ga haka an kashe mutum guda daga cikin masu zanga-zanga a ƙauyen Nawa dake kudancin Deraa, da ma dai ƙarin mutum guda a arewa maso yammacin gundumar Idlib, lamarin da ya sanya dubun-dubatar 'yan ƙasar gudanar da zanga-zanga a wurare da dama.
Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan fara aiki da shirin wanzar da zaman lafiya da manzon musamman na Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Anan ke jagoranta.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Mohammad Nasir Awal