1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici ya kai ga hallakar fiye da 100 a Darfur

May 3, 2013

Tun ba yau ba ƙabilun Gimir da na Beni Halba ke rikici kan mallakan filaye a yankin kudancin Darfur. Ana zargin gwamnatin kasar ne da asasawa

https://p.dw.com/p/18Rgq
** FILE ** In this Friday, Sept. 14, 2007 file photo, Sudanese President Omar al-Bashir is seen in Rome, Italy. Prosecutor Luis Moreno-Ocampo asked a three-judge panel at the International Criminal Court to issue an arrest warrant for President Omar al-Bashir on genocide charges Monday July, 14, 2008, accusing him of masterminding attempts to wipe out African tribes in Darfur with a campaign of murder, rape and deportation. (AP Photo/Gregorio Borgia, File)
Shugaban kasa Omar Al-BashirHoto: AP

Fiye da mutane 100 suka hallaka ɓayan ɓarkewar rikicin ƙabilancin baya-bayan nan a yankin Darfur da ke yammacin Sudan.

Ɗaya daga cikin shuwagabanin ƙabilun da suka yi artabun ya faɗawa kamfanin dillancin labarun Faransa cewa an yi ta faɗa har cikin daren jiya, abunda yayi sanadiyyar mutuwar mutane 37.

Shugaban ƙabilar wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce faɗar ta yi mafari ne daga wata rashin mafinta da aka samu lokacin da ake neman sassanta wani rikicin filayen noma.

Tun ba yau ba ƙabilun Gimir da na Beni Halba ke rikici kan mallakan filaye a yankin kudancin Darfur.

Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya da ke kula da harkokin zamantakewar ɗan adam ta zargi gwamnatin ƙasar da alhakin ingiza faɗa tsakanin ƙabilun biyu rikicin da hukumar ta ce ya ƙi ci yaƙi cinyewa.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba

Edita:            Umaru Aliyu