Rikici ya barke a Masar
May 2, 2012Wasu mutane wadanda ba'a san ko su wanene ba dauke da sanduna da kulake sun afkawa ayarin mutanen da ke zanga zangar adawa da mahukuntan mulkin sojin a wajen ma'aikatar tsaro dake birnin Alkahira. Mutane akalla 20 aka bada rahoton sun rasu yayin arangamar wasu da dama kuma sun jikata. Tun a ranar Asabar din da wuce magoya bayan dan takarar jam'iyyar Salafiyya Hazem Abu Ismail suka yi gangamin zaman darsham na har sai baba ta gani, bayan da hukumar zabe ta haramtawa fittacen dan takararta tsayawa takara a zaben shugaban kasar da za'a yi nan gaba a cikin wannan watan. Jam'iyyar yan uwa musulmi wadda ke da kusan rabin wakilai a majalisar dokoki ta kauracewa taron da majalisar sojin kasar ta kira domin nuna bacin ranta ga wannan abin da ya faru. Shima a nasa bangaren dan takarar jam'iyyar ta Muslim Brothers Mohammed Mursi yace zai dakatar da yakin neman zabe na kwana biyu domin nuna juyayi ga mutanen suka rasu da kuma wadanda suka sami raunuka.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Usman Shehu Usman