Rikici tsakanin Siriya da Turkiyya ya fara shafar Rasha
October 11, 2012Hukumomi a ƙasar Turkiyya sun saki jirgin fasinjar Rasha da ke kan hanyarsa ta zuwa Siriya bayan da mahukunta a birnin Ankara fadar gwamnatin Turkiyya suka yi anfani da wasu jiragen yaƙi biyu domin tilastawa jirgin sauka a birnin bisa zargin yana ɗauke da makamai zuwa Siriya. Ministan kula da harkokin wajen Turkiyya Ahmet Davutoglu yace akwai wasu kayayyakin da jami'an Turkiyya suka ƙwace daga cikin waɗanda jirgin ke ɗauke da su, amma ba tare da ya bayyana nau'in kayayyakin ba.
Rasha dai ita ce babbar ƙasar da ke samarwa Siriya makamai, kuma sau ukku tana hawan kujerar naƙi dangane da ƙudirin sanyawa gwamnatin shugaba Assad takunkumi a kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya. Tilastawa jirgin na Rasha ya sauka shi ne jerin taƙaddama na baya bayannan da ke yaɗuwa a tsakanin ƙasashen duniya sakamakon rikicin ƙasar Siriya.
A cikin tsukin mako guda kuma Turkiyya da Siriya sun yi ta musayar harbe-harben makaman roka ta kan iyakokin su, inda babban hafsan sojin Turkiyya yayi gagaɗin cewar Turkiyya za ta mayar da martani mai tsanani muddin dai aka ci gaba da jefa makamai a cikin yankunan ta.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu