1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Habasha: Rikici na kara kazanta

Lateefa Mustapha Ja'afar
November 19, 2020

Dubban mutane na ci gaba da tserewa rikici a kasar Habasha, yayin da ake ci gaba da bayyana fargaba kan cewa fadan da ake gwabzawa tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawayen Tigray ka iya bazuwa zuwa kasashe makwabtanta.

https://p.dw.com/p/3laCX
Symbolbild Hunger Übersättigung Ungleiche Verteilung von Lebensmitteln
Ana fargabar 'yan gudun hijirar Habasha za su fada halin taskuHoto: Michael Gottschalk/photothek/imago images

Abun damuwa yanzu shi ne halin tagayyara da mutanen da ke tserewa suka tsinci kansu. Dubbai na cikin kunci kamar yadda Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa a gaggauta tsagaita bude wuta domin shawo kan fadan da ke barazana ga rayuwar miliyoyi. 

A yayin da al'umma ke ci gaba da galaibata, a nata bangaren gwamnatin Habashan ta ce nan ba da jimawa ba za ta yi galaba kan 'yan tawayen domin kuwa dakarunta sun karya lagonsu. Hukumar Kula da 'yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniyar dai, ta kuma koka kan halin da rikicin ya fara jefa rayuwar farafen hula.

Ana dai fargabar cewa fadan ka iya rikidewa zuwa yakin basasa, inda dubbai al'ummar Habashan suka tsere zuwa Sudan da ke makwabtaka da kasar, lamarin da ake fargabar cewa zai yi illa ga kasashen biyu. Tuni ma dai kasar Iritiriya ta fara karbar nata kason a wannan rikici, inda 'yan tawayen na Tigray suka kai wasu hare-hare kan filin jiragen samanta na Asmara babban birnin kasar.