1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici kan iyakar Yuganda da Kongo

August 3, 2012

Hukumomin Yuganda sun ɗauki matakan riga-kafin rikice-rikice a kan iyakarsu da Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo.

https://p.dw.com/p/15jlX
(100302) -- BUDUDA(UGANDA), March 2, 2010 -- Residents gather around a rescue helicopter at an open ground after a landslide in Nametsi Village in Bududa District, eastern Uganda, on March 2, 2010. Rescue workers recovered 55 bodies as of noon on Tuesday after the Monday night mudslide covering an area of 200 meters wide came down and buried three villages in eastern Uganda. More than 300 people are still missing and 31 survivors had been accounted for. Apollo Mukhwana) (zw)
Hoto: picture-alliance/Photoshot

Hukumomin a kasar Yuganda sun bada sanarwar kulle kan iyakar ƙasar da Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo bayan wani faɗan da ya barke kan iyakokin kasashen biyu tsakanin mayakan ƙungiyar Mai-Mai da dakarun gwamnatin Kongo a yankin Kisandi da ke arewacin kasar. A cewar wani gidan rediyon kongo mai zaman kansa,wasu mutane dauke da makamai daga yankin Ruwenzori ne suka kai hari ga wani ofishin 'yan sandan da kuma ofishin shari'ar garin. To sai dai bayan sa'o'i a na bata-kashi tsakanin ɓangarorin biyu, dakarun gwamnatin sun samu nasarar kwace ofisoshin daga hannun 'yan tawayen.

Wani mai magana da yayun ministan harakokin cikin gidan Yuganda ya ce gwamnatin ta ɗau wannan matakin ne don kaucewa abun da ka iya biyo baya.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Mohamad Nasiou Awal