Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya cikin rikici
December 23, 2020Yanzu haka dai, ana gwabza fada tsakanin kungiyoyin tawaye da dakarun gwamnati da na Majalisar Dinkin Duniya a birnin Bambari da ke tsakiyar kasar. Tuni dai 'yan adawar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar suka bukaci da a dage zabe, yayin da al'ummar kasar da ma kasashe makwabta ke nuna fargaba dangane da tashe-tashen hankulan. Sa'o'i da dama aka shafe ana arangama tsakanin kungiyoyin tawayen da dakarun gwamnati a garin na Bambari da ke da tazarar kilometa 380 da Bangui babba birnin kasar.
Karin Bayani: Nasara kan kungiyoyin 'yan bindiga a Afirka ta Tsakiya
Hasali ma garin da ke zama na hudu a girma, sai da ya fada hannun masu tayar da kayar baya, kafin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar su sake kwato shi. Ko da yake dai rundunar kiyaye zaman lafiyar ta MINUSCA ta bayyana cewa kura ta lafa a garin na Bambari, amma a garin Bossambele da ke da nisan kilometa 152 da birnin Bangui, sassan da ke rikici da juna na tafka kazamin fada tsakaninsu.
Duk da cewa babu alkaluma dangane da yawan wadanda suka rigamu gidan gaskiya, amma kuma sojoji da suka ji rauni a Bossambele na tururuwa a babban asibitin Bangui. Wannan ne ma ya sa 'yan kasar fadawa cikin damuwa ba, saboda tashe-tashen hankula sun bazu zuwa wasu sassa na kasar. Tuni ma wasu al'ummar kasar suka fara danganta abin da ke faruwa da rikicin da ya faru a 2012-2013 wanda ya kai ga hambarar da Francois Bozize tare da jefa kasar cikin yakin basasa. Saboda haka ne wasu ke ganin cewa da kamar wuya a gudanar da sahihin zaben 'yan majalisa da na shugaban kasa a ranar Lahadi mai zuwa
Karin Bayani: Taron neman zaman lafiya
Kawunan 'yan takarar a tagwayen zabukan sun rabu biyu: Wasu na fatan ganin a dage zaben har sai komai ya daidaita, yayin da gwamnati ke ci gaba da nacewa kai da fata sai an gudanar da shi a ranar da aka tsara. Su kuwa kasashen Rasha da Ruwanda suna kai wa Shugaba Archange Touadera goyon bayan sojoji domin ya yi nasarar murkushe 'yan tawaye da ke da daurin gindin tsohon shugaban kasa Francois Bozize. Wannan ne ya sa gwamnatin jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ke zarginshi da zama kanwa uwar gami na rikice-rikicen da ake fama da su, inda ta bayyana cewa Bozize ya kudiri aniyar amfani da 'yan tawaye wajen ha,barar da gwamnatin farar hula.
Kasashen da ke makwabtaka na nuna damuwa dangane da rikicin da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ke fama da shi, amma ko daya daga cikinsu kowa da bangaren da yake marawa. Sai dai Jean-Jacques Wondo na cibiyar nazarin lamuran tsaro da siyasa a yankin Tsakiyar Afirka, ya ce sarkakiyar da ke tattare da rikicin Afirka ta Tsakiyan kowa na neman tasa ta fisshe shi: "Imma Shugaba Denis Sassou N’guesso ne ko ko Shugaban Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango Félix Tshisekedi ne, a fakaice suna kokarin wakiltar Faransa wajen neman sansanta rikicin, don kalubalantar kasancewar sojojin Rasha a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya."
A yammacin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, wasu kungiyoyin tawaye uku da suka kulla kawance tsakaninsu sun datse muhimmiyar hanya da ake amfani da ita wajen shigar da kayayyakin bukatun yau da kulum a Bangui baban birnin kasar.