Rikici akan makomar tsohon shugaban Masar
July 28, 2011Kamfanin dillancin labaran ƙasar Masar ya sanar da cewar a ranar ukku ga watan Agustan dake kamawa ne za'a gudanar da shari'ar tsohon shugaban ƙasar Hosni Mubarak a birnin alQahira na ƙasar. Tsohon shugaban, wanda zanga-zangar neman sauyin ta tilasta masa sauka daga mulki, yana kwance ne a gadon asibiti dake birnin Sharm el-Sheikh, inda yake karɓar jiyyar da ta shafi bugun zuciya.
Sauya masa wurin shari'a zuwa birnin na alQahira, na daga cikin manyan buƙatun masu zanga-zangar da ta samar da juyin juya hali a ƙasar, waɗanda suke zaman doya da manja da hukumomin sojin dake tafiyar da harkokin mulki a ƙasar bayan hambarar da shugaban, wanda ya haɗa da zargin da suke yiwa sojojin cewar suna jinkirta gurfanar da tsoffin jami'an gwamnatin ƙasar.
Tsohon shugaba Mubarak - mai shekaru 83 da haihuwa dai zai fuskanci shari'a ne tare da 'ya'yan sa guda biyu, da kuma tsohon ministan kula da harkokin cikin gida a ƙasar Habib al-Adli, waɗanda ke jiran shari'a a wani gidan yarin dake birnin na alQahira.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Ahmad Tijani Lawal