1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Rikice-rikice na hana yara zuwa makaranta

Suleiman Babayo AH
September 9, 2024

Rikice-rikice da matsalolin tattalin arziki suna kan gaba wajen hana milyoyin yara zuwa makaranta a yankuna tsakiya da yammacin nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/4kRGk
Wata makaranta a kasar Kamaru
Wata makaranta a kasar KamaruHoto: Tamfu Ciduan Ndimbie/My Media Prime TV/Reuters

Kimanin yara milyan uku a kasashen yammaci da tsakiyar Afirka ba sa iya zuwa makaranta sakamakon rikice-rikicen da ke faruwa a yankunan. Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da makarantu dubu-14 aka rufe a zangon farko na wannan shekara ta 2024 cikin kasashe 24 na yankunan biyu.

Karin Bayani: Najeriya: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da daliban jami'a

Haka ya nuna cewa alkaluman sun haura na bara da fiye da dubu-daya. Kasashen Burkina Faso, da Mali, da Kamaru, gami da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango suke kan gaba na matsalolin da ake fuskanta.

Majalisar Dinkin Duniya ta kara da cewa yara kimanin milyan-57 da ya dace ace suna zuwa makaranta tsakanin shekara 5 zuwa shekaru 14 na haihuwa a kasashen na yammaci da tsakiyar Afirka ba sa zuwa makaranta. Rikice-rikice da da matsalolin tattalin arziki ke kan gaba wajen haddasa matsalolin rashin zuwa makaranta a yankunan da ke nahiyar Afirka.