Rikice-rikice ka iya rusa Masar
January 29, 2013A wannan Talata, babban habsan sojan ƙasar Masar ya yi gargadin cewa rikice-rikicen siyasan da ƙasar ke fuskanta ka iya durƙusar da ita baki daya. Wannan yayin da dubban mutane su ka yi fatali da dokar hana fita da aka kafa cikin wasu birane, kuma mutane kimanin 52 su ka hallaka kawo yanzu.
Janar Abdel Fattah al-Sissi wanda kuma shi ne ministan tsaro, ya ce, tashin hankalin da ƙasar ke fuskanta na siyasa da tattalin arziki za su iya wargaza ƙasar da kuma barazana da al'uma ta gaba ɗaya.
Cikin ƙarshen mako Shugaban ƙasar ta Masar Mohamed Mursi ya aiyana dokar ta ɓaci cikin birane uku na Port Said, Ismailiya da Suez. Kuma ranar Litinin Majalisar Dattawa ta amince da matakin. Amma mutane na ci gaba da bijirewa dokar cikin waɗannan birane.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Yahouza Sadissou Madobi