1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Riikicin ƙasar Siriya na ƙara jan hankali ƙasashen duniya

July 18, 2011

Ƙasashen Ƙungiyar Tarrayar Turai na shrin ƙara saka takunkumi ga ƙasar Siriya

https://p.dw.com/p/11z2I
Masu zanga zangar nuna ƙin jinin gwamnatin a SiriyaHoto: picture alliance/dpa

Ministocin harkokin waje na ƙasashen Ƙungiyar Tarrayar Turai da ke gudanar da taro a birnin Brussels na ƙasar Beljium sun yi kira da babbar murya da a kawo sauyin gwamnatin Bashar Al-Assad a ƙasar Siriya wacce dakarunta ke ci-gaba da fatattakar al'umma da ke yin zanga zangar ƙin jinin gwamnati.

Tun da farko dai daga cikin matakai na matsin lamba da ƙasashen ƙungiyar Tarrayar Turai ke son ƙara ƙaƙabawa ƙasar ta Siriya, hada yiwuwar ƙara saka takunkumin karya tattalin arziki ga ƙasar da kuma shugabanninta. Dama dai tun can da farko ƙungiyar ta EU ta amince da wasu jerin takunkumi har guda ukku ga wasu shugabannin ƙasar ta Siriya da kamfanoni da kuma manyan sojoji waɗanda ke taimaka wa gwamnatin wajan gallaza wa 'yan adawa, Takunkumin dai ya haɗa ne da na hana taɓa ajiyar kuɗaɗen a cikin bankuna na waje .Guido Westerwelle ministan harkokin waje na ƙasar Jamus cewa ya yi:

'' Mun riga mun ƙare da maganar takunkumi a yanzu muna kan maganar ƙara matsa ƙaimi ga gwamnatin kuma ya kamata mu yi baki ɗaya . zancen da na yi kenan da ministan harkokin waje na ƙasar Rasha Sergej Lawrow':'

Ministocin baki ɗayansu sun yi amannar cewa dole shugaba Bashar Al-Assad ya fice daga mulkin domin bai wa yan ƙasar Siriya damar yanke shawara ga zaɓi na dimokaraɗiyya, ko da shi ke wasu daga cikin ministocin na yunƙurin cewa ko dai Bachar Al-Assad ɗin ya yi koskorima ga gwamnatinsa domin kawo canje canje,to amma wasu masu zazzafan ra'ayi irin su ministan harkokin wajen na ƙasar Sweden, Carl Bildt cewa yake yi ba magana ba ce ta mutun ɗaya ba, magana ce ta gwamnati. Ya ce tilas ne wannan gwamnati ta sauka domin ba da wuri ga wata sabuwar gwamnati dangane da yadda mutuncinta ya faɗi a idon ' yan ƙasar da kuma duniya baki ɗaya.

ƙasashen na tunani yin aiki tare da ƙungiyar ƙasashen Larabawa da kuma ƙasar Turkiya domin kai ga hana gwamnatin Siriya yin amfanin da sojoji domin kashe masu yin bore. Catherine Asthon ita ce babbar kantomar ƙungiyar Tarrayar Turai kan manufofin ƙetare ta kuma baiyana cewa sun yi tsari .

''Ta ce ina tsamanin abin da ya kamata Ƙungiyar Tarrayar turai ta yi ta riga ta yi shi. Muna da wata tawaga dake a ƙasar ta Siriya ta na aiki da dakarun tsaro suna magana da al'umma ta yadda za a iya dakatar da aikta kisan gilla akan fararan fula.''Rahotannin da ke zuwa mana na cewa mutane aƙalla guda 30 suka rasa rayukansu a wani faɗan da aka gwabza tsakanin magoya bayan shugaban ƙasar da na yan adawa a garin Homs,yayin da kuma jami'an tsaro suka riƙa yin kutse a cikin gidajen jama'a a garin Zabadani dake a yankin kudanci da kuma birnin na Homs inda suka kama mutane guda 50

ƙasar ta Siriya ta na fama da tashe tashen hankula tun watannin fuɗu da suka wucce wanda kawo yanzu aka ƙiyasta cewa mutane 1,400 suka mutu yayin da ake tsare da wasu sama da 12,000 a gidajen kurku baya ga wasu dubbai da suka yi gudun hijira.

Daga ƙasa za a iya sauraron sautin wannan rahoto

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Halima Balaraba Abbas