1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rigingimun Sudan da Kudancin Sudan

April 16, 2012

Talakwan da ke kan iyakan jamhoriyar Sudan da Kudancin Sudan sun shiga mawuyacin hali sakamakon yawan rigingimu da rashin abinci

https://p.dw.com/p/14exY
Copyright: Jared Ferrie, freier DW-Mitarbeiter, Süd-Sudan, Januar 2012
Hoto: DW

Masu aikin agaji sun ce rigingimun da ke afkuwa tsakanin Sudan da Kudancin Sudan na cigaba da ta'azara abun da ke tasiri kan yanayin zamnatakewar talakawan da ke kan iyakan. Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce akalla yan gudun hijira 400 ke kwarara a sansanin Yi-da da ke kudancin Sudan kowace rana.

Jiragen yakin Sudan na cigaba da luguden wuta kan yankunan da ke kudancin tun bayan da fadan ya karu sakamakon kutsen da Kudancin Sudan ta yi a garin Heglig mai rijiyoyin man fetur. A waje guda kuma majalisar dokokin sudan ta ce ta mayar da Kudancin Sudan abokiyar gabarta.

'Yan majalisan sun yanke wannan shawara ce bayan da suka kada kuri'a akan matakin da zasu dauka kan makociyar tasu, bayan da dakarunta suka mamaye filayen manta. haka nan kuma Kudancin ta zargi gwamnatin Khartoum da alhakin hare-haren da suka kai ga hallakar fararen hula 10 a kasar, wanda kuma ya shafi wani sansanin dakarun wanzar da zaman lafiyan Majalisar Dinkin Duniya.

Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Zainab Mohammed Abubakar