1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rigingimu sun dabaibaye zaben kasar Mali

Abdul-raheem Hassan MNA
July 29, 2018

An samu tashe-tashen hankula a wasu sassan kasar Mali a daidai lokacin da ake gudanar da babban zaben kasar a wannan Lahadi.

https://p.dw.com/p/32H1j
Mali Wahlen
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

'Yan bindiga a Mali sun harba makaman roka kan wata cibiyar rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, wato MINUSMA da ke kasar, a daidai lokacin da ake gudanar da babban zabe a kasar ta Mali.

Babu dai rahotannin asarar rayuka daga jerin hare-haren, sai dai kona wasu rumfunan zabe da akwatunan zabe a wasu yankuna ya hana gudanar da zaben a wurare da dama musamman a arewacin kasar.

Sai dai Baba Moulaye Haidara, na wata kungiyar farar hula a garin Timbuktu, daya ne a cikin masu sa ido a zaben, ya shedawa tashar DW cewa ba a samu wani hargitsi a yankinsu ba.

"A garin Timbuktu komai na tafiya salin alim, jama'a sun kada kuri'a cikin tsanaki ba da wata matsala ba. Ba mu kuma samu wani labari game da aringizon zabe ba, duk wanda ya kada kuri'a a nan yana da katin zabe."

Shugaba Ibrahim Boubacar Keita mai shekaru 73, na cikin 'yan takara 24 cikin har da mace guda da ke fafatawa a zaben na wannan Lahadi mai cike da fatan samun shugaban da zai kawar da matsalolin tsaro da tattalin arziki da kasar ke ciki.