1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

EU ta samar da riga-kafin kyandar biri

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 26, 2022

Kasashen kungiyar Tarayyar Turai EU ka iya fara amfani da allurar riga-kafin cutar agana, domin magance cutar kyandar biri da dangoginta.

https://p.dw.com/p/4EeIW
WHO | Hukumar Lafiya ta Duniya | Imvanex | Agana
allurar riga-kafin cutar agana, za ta iya yin riga-kafin cutar kyandar biriHoto: Michael Bihlmayer/CHROMORANGE/picture allianc

Kamfanin sarrafa magunguna na kasar Denmak mai suna Imvanex Bavarian Nordic ya tabbatar da cewa, a yanzu za a iya amfani da allurar riga-kafin agana ta kamfanin wato Imvanex a kasashen Tarayyar Turai EU domin magance cutar kyandar birin da dangoginta. Wannan dai na zuwa ne, bayan kasashen Kanada da Amirka sun bayyana amincewarsu da allurar riga-kafin aganar a matsayin ta kyandar birin. A karshen mako ne dai, Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ayyana cutar a matsayin wadda ke bukatar daukin gaggawa a duniya. Tuni dai cutar kyandar birin ta zama gama-gari a kasashen yammaci da tsakiyar Afirka, kafin daga bisani ta fara bazuwa a duniya cikin watan Mayun wannan shekara. Hukumar ta WHO ta tabbatar da cewa, sama da mutane dubu 15 da 300 ne suka kamu da cutar a kasashe 75 tun bayan bullar ta kana ta fi karfi a kasashen nahiyar Turai.