1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Turkiyya na farfado da guraren ibadar Kiristoci

Zulaiha Abubakar
August 3, 2019

Mabiya addinin Kirista da yawansu yakai dubu 17 za su iya gudanar da ibada a cocin Istanbul da zarar an kammala gini.Shugaba Erdogan ya ce alhakin gwamnati ne ta samar wa Kiristocin Turkiyya muhallin gudanar da ibada. 

https://p.dw.com/p/3NIGQ
Türkei Wahlen Wahlkampf Recep Tayyip Erdogan
Hoto: Reuters/M. Sezer

 

Duk da zargin gwamnatin kasar Turkiyya da yunkurin mayar da kasar ta addinin Islama gabadaya, shugaba Erdogan na aikin budewa da kuma farfado da guraren ibadar Kiristoci tare da gargadin jama'a da su guji cutar da wani bangare na al'ummar kasar. Wani sakamakon kidaya na baya-bayan nan a kasar ta Turkiyya ta tabbatar da kaso 98 na al'ummar kasar mabiya addinin Islama ne.


Wannan shi ne karon farko da shugaba ya aza ginin irin wannan katafariyar Coci a birnin Istanbul na kasar Turkiyya tun a Tshekara ta 1923.