1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Real Madrid ta lashe kofin kungiyoyin duniya

Mouhamadou Awal Balarabe RGB
February 13, 2023

Real Madrid ta lashe kofin duniya na kungiyoyin kwallon kafa a karo na 100 a yayin da Bayern Munich ta ci-gaba da fuskantar barazana daga Union Berlin.

https://p.dw.com/p/4NQjI
Real Madrid ta lashe kofin FIFA na kungiyoyi
Real Madrid ta lashe kofin FIFA na kungiyoyiHoto: KHALED DESOUKI/AFP

Real Madrid ta Spain ta samu nasara a kan kungiyar Al-Hilal ta kasar Saudiyya da ci 5-3 a ranar Asabar da ta gabata a wasan karshe na cin kofin duniya na kungiyoyin kwallon kafa wanda Maroko ta dauki bakunci. 

Duk da cewa wannan shi ne karon farko da 'yan Saudiyya ke buga wasan karshe, amma dai 'yan wasan koci Carlo Ancelotti sun nuna musu cewa, ruwa ba sa'an kwando ne musamman ma a fannin yawan kai hari Godiya ma ta tabbata ga Vinicius Junior da Federico Valverde da suka ci kwallaye biyu, da kuma Karim Benzema da ke rike da kyautar Ballon d'Or Faransanci. Amma dai kungiyar Al-Hilal ta nuna kwarin gwiwa inda ta zura kwallaye uku ta hannun Moussa Marega da Luciano Vietto da ya ci kwallaye biyu. 

Kungiyar ta Madrid babban birnin Spain ta kasance mafi samun nasara a tarihin gasar cin kofin kungiyoyi kwallon kafa na duniya. Hasali ma dai wannan shi ne karo na biyar da ta yi cara baya ga shekarun 2014 da 2016 da 2017 da 2018, kuma wannan shi ne kofi na 100 da Real ta lashe a tarihinta na kwallon kafa a dukkan gasanni. Ko a yanzu ma ita ce ke rike da kofin kwallon kafa na zakarun Turai wati Champions League. Sai dai Fifa ta sanar da cewa za ta sauya fasalin gasar kungiyoyi nan da shekaru uku masu zuwa domin bai wa wakilan kasashe 32 damar karawa duk bayan shekara hudu.

A confederation cup kuwa, Kungiyar Diables Noirs ta Kwango Brazaville ta samu nasara a kan Rivers United ta Najeriya ci 3-0 a wasan farko na gasar neman cin kofin gasar confederation Cup. Ita kuwa ASEC Mimosas da DC Motema Pembe na DR Kwango sun tashi canjaras a daya wasan da suka buga a rukunin B. Ita kuwa US Monastir ta Aljeriya ta doke Young Africans ta Tanzania da ci 2-0. Wannan nasarar ta sa ta samun matsayi na biyu a rukunin D bayan TP Mazembe ta Kwango wacce ta doke Real Bamako da ci 3-1. A nata bangaren Future FC ta Masar ta tashi kunnen doki 1-1 a lokacin da ta kalubalanci AS Kara ta Togo. 

A gasar Bundesliga, Bayern Munich a karawa da ta yi da Bochum musamman a farkon rabin lokaci, ba ta yi katabusa ba, amma dai 'yan wasanta sun yi aikin da ya dace wajen samun nasara da ci 3-0 a kan Bochum tare da ci gaba da jan zare a saman teburin Bundesliga da maki 39. Wannan ne karo na biyu a jere da Bayern ta samu nasara a gasar Bundesliga a wannan shekara ta 2023. Thomas Müller da Kingsley Coman da Serge Gnabry ne suka zura kwallaye uku a wasan mako na 20.

Karawar Bayern Munich da Bochum
Karawar Bayern Munich da BochumHoto: Andreas Schaad/AP Photo/picture alliance

A yanzu Bayern Munich na mayar da hankali kan karawar da za ta yi da PSG a daren Talata a gasar zakarun Turai. Amma Leon Goretzka ya ya intifakin cewa dole ne sun inganta wasansu idan sun son doke Paris. Sai dai a wannan karon Bayern ba ta tabbacin zama zakara domin Union Berlin na ci-gaba da caccakar dunduniyarta sakamakon bin RB Leipzig har gida da ta yi kuma ta lallasa ta da ci 2-1. A yanzu dai ratar maki daya ne ke tsakanin Bayern da Union. sai dai Borussia Dortmund na ci gaba da kwanton bauna a matsayi na uku bayan da ta doke Werder Bremen da ci 2-0. 

A kasan teburin Bundesliga kuwa, Hertha Berlin ta cire wa kanta kitse a wuta, inda ta samu nasara da ci 4-1 a fafatawar da ta yi da Borussia Mönchengladbach, lamarin da ya bata damar komawa matsayi na 16 da maki 17. Ma'ana da maki daya ta sha gaban VfB Stuttgart wacce ya sake faduwa a gaban Freiburg. A nata bangaren, Schalke 04 da ke zama 'yar baya ga dangi ta tashi 0-0 da Wolfsburg.

A sauran manyan lig na kasashen Turai, sakamakon wasu wasanni sun bada mamaki musamman a Faransa rashin nasara da PSG da ke saman teburi na lig kwallon kafar Faransa ta yi a filin na Monaco inda aka lallasata ta ci 3-0. Wannan dai ba ya rasa nasaba da rashin halartar wasan da taurarinta Mbappe da Messi da Mukele da Verati ba su yi ba. Sai dai nasarar da Marseille ta samu a kan Clermont da ci 2-0 ya sa ratar maki biyar ne kadai ke tsakanin abokan hamayyar biyu.

Fafatawa a tsakanin ManU da Leeds
Fafatawa a tsakanin ManU da LeedsHoto: Malcolm Bryce/imago images/Pro Sports Images

A Premier League na Ingila kuwa, Manchester United ta doke Leeds United 2-0 a wasan mako na 23, kuma godiya ta tabbata ga Marcus Rashford da ya fara cin kwallo a minti na 80, wanda ya sa shi zama dan wasa da ya fi zura kwallaye a raga tun bayan da aka kammala gasar kofin duniya. A nata bangaren kuwa, Manchester City ta lashe karon batta da ta yi da Aston Villa da ci 3-2, yayin da aka tashi babu yabo babu fallasa 1-1 a karawa da aka yi tsakani Arsenal Brendford. 

A La Liga kuwa, Barcelona ta bi Villerrial har gida kuma ta doke ta da ci daya mai ban haushi, lamarin da ya bata damar ci gaba da zama a saman teburin lig don kasar Spain tare da yi wa Real Madrid ratar maki tara.

Kansas City ta lashe gasar Super Bowl
Kansas City ta lashe gasar Super BowlHoto: Mark J. Rebilas-USA TODAY Sports

A Amirka kuma, a daren ranar Lahadin da ta gabata, kungiyar wasan dauki kwallo ka ruga da gudu da aka fi sani da American Football ta Kansas City Chiefs ta yi galaba a kan kungiyar Philadelphia Eagles da maki 38 da 35 a gasar cin kofin kasa da aka fafata a jihar Arizona. Koda yake Philadelphia ta fara wasan da kafar dama har zuwa hutun rabin lokaci tana kan gaba, amma daga bisani Kansas ta yunkuro, har a kai ga yi kiki-kaka da maki 35- kowane. Sai da ya rage wasu ‘yan dakikoki a kammala wasan ne tukuna Kansas ta samu bugun fenarati wanda hakan ya sa ta lashe kofi.

A fagen dambe MMA, inda Islam Makhachev dan kasar Rasha ya doke babban abokin hamayyarsa dan kasar Australia Alexander Volkanovski a ranar Lahadi a birnin Perth, lamarin da ya ba shi damar ci gaba da rike kambunsa a ajin mara nauyi. Wannan dai shi ne karon farko da dan damben na Rasha mai shekaru 31, ya kare matsayinsa tun bayan da ya kwace wannan kambu a hannun Charles Oliveira na Brazil a watan Oktoban da ya gabata. Sai dai a nasa bangaren Volkanovski ya kasa cika burinsa na zama dan damben UFC na farko da zai rike kambun zakara na biyu a lokaci guda, wato na ajin marasa nauyi da na ajin 'yan dagaji da yake rike da shi a yanzu.