1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara harkoki a garin da Corona ta fara bulla

March 30, 2020

Masu shaguna sun bude kasuwancinsu a wannan Litinin a birnin Wuhan na kasar China, inda cutar Corona ta fara bulla.

https://p.dw.com/p/3aBFy
China | Coronavirus | Rückkehr zur Normalität
Hoto: picture-alliance/Xinhua/S. Bohan

Kimanin watanni biyu ne dai aka kwashe shaguna a kulle saboda dokar zama a gida da hukumomin China suka sanya a wannan yanki domin takaita yaduwar cutar Corona.

A wannan yanki ne dai Coronavirus ta fara bulla a watan Disambar da ya gabata, daga nan kuma ta bazu a sassa dabam-dabam na duniya har ta kai ga yanzu kasashe kusan 200 ne ke fama da cutar. 

Wata mata mai shago a yankin na Wuhan ta shaida wa 'yan jarida cewa ta yi farin ciki da bude shaguna da aka yi, ta ce ta ji kamar it yi kuka saboda jindadi.

Rahotanni sun ce kusan kashi 70 zuwa 80 cikin 100 na shaguna a yankin na Wuhan sun bude a safiyar Litinin din nan. Sai dai sun kayyade yawan adadin mutanen da za su iya shiga shagunan sayayya a lokaci guda.

Kazalika a ranar Lahadin nan hukumomi sun dawo da sufurin motocin safa-safa da kuma jirgin kasa a garin na Wuhan. Tun a ranar 23 ga watan Janairu hukumomi suka rufe harkar sufuri, inda akalla mutane milyan 11 suka daina zirga-zirga saboda matakin rage yaduwar cutar da hukumomi suka dauka.