1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rawar da ƙungiyar ƙawance ta NATO za ta taka a rikicin Libiya

March 23, 2011

ƙungiyar ƙawance ta NATO ta goyi bayan ƙarfafa haramcin makaman da aka yi wa Libiya kuma ta ce za ta ƙara ƙarfafa ƙudurin MDD na haramata shawagin jiragen yaƙi

https://p.dw.com/p/10gE5
Shelkwatar NATOHoto: AP

Faransa ta cimma wata yarjejeniya da Amurka da Burtaniya, inda ta amince da ƙungiyar ƙawance ta NATO ta taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da ƙudurin Mjalisar Ɗinkin Duniya na haramata shawagin jiragen yaƙi a Libiya. Wannan sanarwar ta biyo bayan wata tattaunawar da ta gudana tsakanin Shugaba Obama na Amurka, da Frime Ministan Burtaniya David Cameron da shugaba Nicolas Sarkozy na Faransa. Amma ƙawayen ba su zartar ko ƙungiyar ta NATO za ta jagoranci ƙudurin a siyasance ba.

A babban birnin Brussels, ƙungiyar ƙawance ta NATO ta goyi bayan ƙarfafa haramcin makaman da aka yi wa Libiya kuma ta ce za ta ƙara ƙarfafa ƙudurin MDD na haramata shawagin jiragen yaƙi a sararin samaniyar Libiyar idan har ya kama. Ko da yake dai rashin amincewar Faransa da Turkiya ya ƙara ketsa kutungwuilar sanya wannan ƙudurin a ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar ƙawancen ta NATO. Kawo yanzu dai akwai damuwar cewa barin ƙungiyar ƙawance ta NATOn ta jagoranci aiwatar da ƙudurin ba zai sami karɓuwa ba a ƙasashen larabawa.

Dakarun gwamnatin Libiya dai, sun cigaba da kai hari a yankunan da ke ƙarƙashin jagorancin 'yan tawaye, duk da luguden wutan da ƙasasshen ƙetare ke kai masu. An yi ruwan harsashai da makamai masu linzami a garuruwan Misrata da Sinatan, kuma rahotanni daga kafafen yaɗa labarai sun ce mutane da dama sun jikkata.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar