1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Damuwa game da shirin gudanar da zabe a Afirka ta Tsakiya

October 30, 2019

Matsalar tsaro da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ke fuskanta na barazana ga shirye-shiryen zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa.

https://p.dw.com/p/3SCCD
Zentralafrikanische Republik Bangui Wahlen Wahllokal
Hoto: picture-alliance/Xinhua

Dukkanin bangarorin siyasa na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun yi amanar cewar matsalar tsaro da kasar ke fuskanta barazana ce ga gudanar da ingantaccen zabe. Amma kuma bambance-bambance na tasowa tsakaninsu idan aka dago batun jinkirin wadannan zabukan. Sai dai a lokacin da yake jawabi a gaban Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, manzon wannan hukuma a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Mankeur Ndiaye bai boye adawarsa da duk wani mataki na dage zaben ba, saboda ita kadai ce hanya mafi a'ala ta tabbatar da mulkin dimukuradiyya da hadin kan 'yan kasa.

"Tabbas jinkiri wajen gudanar da zabubbuka masu zuwa na iya haifar da yanayin kara zube na kasa da ba ta da sahihin shugabanci, kuma zai iya haifar da sabon sauyin siyasa na rikon kwarya wanda, na tabbata, zai iya kawo illa ga tabbatar da dimukuradiyya da dorewar zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya." 

Shugaba Faustin Archange Touadéra na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Shugaba Faustin Archange Touadéra na Jamhuriyar Afirka ta TsakiyaHoto: Getty Images/AFP/S. Kambou

A ranar 15 ga watan Nuwamba ne wa'adin aikin wanzar da zaman lafiya da Majalisar Dinkin Duniya ke yi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ke karewa. Sai dai babban jami'inta, Mankeur Ndiaye ya yi kira ga kasashen duniya da su ba da gudummawar kudade da suka dace don a tsawaita aikin ci gaba da dora kasar kan turba madaidaiciya. Sannan kuma su samar da kudaden gudanar da zabuka masu zuwa. Bisa ga jadawalin da aka fitar dai, zagayen farko na zaben shugaban kasa zai gudana a cikin watan Disamba na shekarar 2020.

Domin ganin cewar komai ya gudana yadda ya kamata ne hukumar zabe ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya  ta fara rajistar masu kada kuri'a tare da fara tanadar da rumfunan zaben da cibiyoyin tattara bayanan zabe. Saboda haka ne Julius Ngouade-Baba da ke magana da yawun hukumar zabe ta kasa, ya ce babu wani dalili da zai sa a nuna damuwa kan gudanar da zaben a kan lokaci.

"Babu shakka akwai 'yan siyasa na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a yau da suke tunanin cewa bisa dalilan tsaro a cikin kasar, ba za mu iya shirya zaben ba. Amma wadannan ba batutuwa ne da muke la'akari da su ba. Idan aka yi la'akari da mizanin shirye-shiryen zabe, babu wani abu da zai iya hana  gudanar da zabuka. "

Anicet-Georges Dologuélé madugun 'yan adawa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Anicet-Georges Dologuélé madugun 'yan adawa a Jamhuriyar Afirka ta TsakiyaHoto: Reuters/S. Modola

Amma madugun adawa na kasar, Anicet Georges Dologuélé ya ce yana da ja a kan wannan batu, inda ya zargi gwamnati da ke ci a yanzu da niyyar gurganta tsarin zaben don kada a gudanar da shi a kan kari.

"Ba na jin za mu iya cewa al'amura suna kan turba madaidaiciya, gwamnatin da ke ci a yanzu ba ta rufa-rufa game da aniyarta ta yin magudin zabe, kuma muna ganin cewa wadannan zabukan idan ba a shirya su da kyau ba, za su haifar mana da rikice-rikice masu wahalar warwarewa, saboda haka kafatanin bagarorin siyasa ne ke nuna damuwa."

Ita ma Kungiyar Tarayyar Afirka na goyon bayan gudanar da zabukan a cikin shekarun 2020 da kuma 2021. Sai dai har yanzu ba a fayyace mataki da za a dauka don ladabtar da duk wanda zai keta yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a birnin  Khartoum ba, wadda ta tanadi gudanar da zaben da zai samu karbuwa a kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.