1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Robert Mugabe na kara jin jiki

Yusuf Bala Nayaya
November 25, 2018

Tsohon shugaban kasar Zimbabuwe mai shekaru 94 ya kai matakin da baya iya tafiya saboda yadda rashin lafiyarsa ke kara tabarbarewa a cewar wanda ya gaji shugaban.

https://p.dw.com/p/38sND
Simbabwe Mugabe bei TV-Ansprache
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Shugaba Emmerson Mnangagwa ya fada wa 'yan jam'iyyar da ke mulki a kasar Zimbabuwe cewa Mugabe na asibiti a kasar Singapor watanni biyu da suka gabata baya iya tafiya sai dai gwamnatin kasar na ci gaba da kula da lafiyarsa.

Tun dai a watan Yuli ne a wani gani da ba kasafai ba, aka ga Mugabe ya fadi lokacin da ya ke gaban na'urar magana a wani taro, kafin daga bisani ya zauna a kan kujera wanda har 'yan jarida suka fita bai tashi daga kujear ba.

Kafin dai tumbuke Mugabe daga kujear mulki a bara ya kasance shugaban kasa mafi yawan shekaru da ya kwashe shekaru 37 a karagar mulkin da a karshe ya jefa kasarsa cikin yanayi na koma bayan tattalin arziki.