1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Karuwar rashin lafiyar kwakwalwa

Rahmatu Abubakar Mahmud RGB
October 18, 2022

An sami karuwar alkaluma na masu fama da rashin lafiyar kwakwalwa a sakamakon matsaloli masu nasaba da yanayin mata bayan haihuwa ko tashin hankali da shaye-shayen miyagun kwayoyi.

https://p.dw.com/p/4IMPj
Indonesien Java Psychiatrie Patienten Fixierung
Hoto: HRW/Andrea Star Reese

A kasar Ghana rahotanin na nuni da cewar an sami ƙarin lamuran lafiyar hankali fiye da yadda ake tsammani, haihuwar ko samun waraka bayan haihuwa tsakanin mata, bakin ciki da shaye-shayen miyagun kwayoyi su ne kan gaba wajen haddasa matsalar rashin lafiyar kwakwalwar.

Asibitin koyarwa na Komfo Anokye kadai ya sami masu tabin hankali sama da dubu bakwai a tsakiyar wannan shekarar idan aka kwatanta da adadin masu cutar dubu shida da aka samu a daidai wannan lokacin a bara. An bayyana hakan ne a yayin wani taro da aka guddanar domin bikin watan Lafiyar kwakwalwa ta duniya.

Hukumar lafiya ta Duniya ta kebe watan Oktoba domin tunawa da kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya a matsayin watan wayar da kan jama'a kan lafiyar kwakwalwa a duk shekara. A wannan karo, kasashe da kungiyoyi za su yi amfani da dabaru daban-daban da suka hada da shirye-shirye don wayar da kan jama'a game da gaskiyar yaduwar rashin lafiyar kwakwalwa a tsakanin al'umma.

Ilimantar da jama'a dai, kamata ya haɗa da yanayi, abubuwan haɗari, jinya da matakan kariya daga cutar. A ganin lokitocin masu Kula da lamuran da suka shafi kwakwalwa, Idan aka sami mutun mai jin daɗin keɓewa wuri guda shi kadai to yana da alaƙa da ɓacin rai da damuwa, waɗanda idan ba a kula da su akan lokaci ba, hakan ka iya haifar da halaye marasa kyau.