1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kasa fahimtar alkiblar sojojin Burkina Faso

Usman Shehu Usman ZUD
October 7, 2022

A cikin dare daya, sunan Ibrahim Traoré ya karade duniya bayan da ya kifar da gwamnati a Burkina Faso. Amma duk da ya yi nasarar karbar mulki, har kawo yanzu an kasa fahimtar alkiblarsa in ji wata jarida a Jamus.

https://p.dw.com/p/4Hum0
Fuskokin matasan sojojin da suka yi juyin mulki a Burkina Faso
Fuskokin matasan sojojin da suka yi juyin mulki a Burkina FasoHoto: Radiodiffusion Télévision du Burkina/AFP

Jaridar Süddeutsche Zeitung ta ce masu juyin mulkin da ba su shirya ba a Burkina Faso sun karbi iko, don haka ne ma dai ba a san manufar sabon shugaban kasar ba. Amma idan da akwai gasar zabar shugaban da ya fi shahara a duniya, Ibrahim Traoré zai samu dama mai kyau. A baya ya kasance kyaftin a cikin sojojin Burkina Faso, ko da shike ba wani matsayi na musamman ba ne. Traoré ya shafe shekaru da dama yana fafatawa da sojojin da ke kan gaba wajen yaki da ta'addancin, amma ko a Ouagadougou babban birnin kasar da wuya wani ya san dan shekaru 34 da haihuwar, sai mako guda da ya wuce, lokacin da aka ji karar farko a ranar Juma'a kuma kwatsam gidan talabijin na kasar ya yi ta watsa shirye-shiryen bidiyo maras lokaci.

''Iritiriya babbar cikas ce ga zaman lafiyar Habasha" in ji jaridar Neue Zürcher Zeitung. Jaridar ta ruwaito William Davison na kungiyar kula da tashe-tashen hankula ta duniya, wanda ya bayyana wanda zai iya matsa lamba kan tattaunawar zaman lafiya a yakin Tigray. Jaridar ta ci gaba da cewa daya daga cikin rikice-rikice mafi muni a duniya ya sake ruruwa bayan tsagaita bude wuta na tsawon watanni biyar. Tun a karshen watan Agusta ne fada ya sake barkewa a yankin Tigray na kasar Habasha. Yanzu haka dai sojojin Habasha da na Iritiriya sun kaddamar da wani gagarumin farmaki kan dakarun 'yan tawayen kabilar Tigray da aka fi sani da TPLF.

Zabe a Lesotho ya kawo tashin hankali. Wannan shi ne sharhin jaridar Die Tageszeitung. Kasar dai ba ta dade da samun kwanciyar hankali ba, amma yankin na samun koma baya. Zaben na wannan Juma'a a Lesotho ya zo daidai da bikin cika shekaru 56 da samun 'yancin kai a wannan mako. Yar mitsitsiyar kasar da ke kan tsaunukan kudancin Afirka da kuma kasar Afirka ta Kudu ta yi kawanya a kowane bangare, ta kasance abin koyi na zaman lafiya da kwanciyar hankali a baya, amma a baya-bayan nan ta zama abin misali na tashe-tashen hankula.

Ku jefar da bindigogin, ku kama alkalami, jaridar Der Spiegel ce ta yi wannan kiran a  labarin Ilwad Elman mai fafutuka, a yayin da ake ba ta lambar yabo ta madadin  kyautar Nobel. Elman, mai shekaru 32, tana kula da cibiyar zaman lafiya da kare hakkin bil'Adama ta Elman a Mogadishu, babban birnin kasar Somalia tare da mahaifiyarta. A watan Nuwamba, dukkansu biyu za su sami lambar yabo saboda aikin da suka yi tare da tsofaffin sojoji da wadanda tashin hankali ya shafa a Somaliya.