1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Putin zai rage luguden wuta a Ukraine

Abdul-raheem Hassan
March 29, 2022

Kasar Turkiyya ta ce an kawo karshen tattaunawar samar da mafita kan rikicin da ke daukar hankalin duniya a gabashin Turai tsakanin kasashen Rasha da Ukraine.

https://p.dw.com/p/49BCk
Ukraine Ukrainische Streitkräfte in Kiew
Hoto: NurPhoto/Jordan Stern/picture alliance

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Turkiyya ta ce an kammala tattaunawar zaman lafiya tsakanin Rasha da kungiyoyin sasantawa na Ukraine da aka gudanar a birnin Santanbul.

Gwamnatin Rasha ta yanke shawarar katse ayyukan dakarunta a kusa da biranen Kyiv da Chernihiv na Ukraine, mataimakin ministan tsaron Moscow Alexander Fomin ya ce sun dauki wannan mataki ne bayan tattaunawar hukumomin kasashen biyu da sukaa yi a birnin Santanbul na kasar Turkiyya don kawo karshen rikicin.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce kimanin mutane miliyan 18 ne a Ukraine za su bukaci agajin gaggawa sakamakon barnar da sojojin Rasha suka haddasa.