1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta soki matsayin ƙasashen yamma a kan rikicin Siriya

July 16, 2012

Gwamnatin birnin Mosko ta zargi ƙasashen na yamma da yin zagon ƙasa domin haddasa wani yakin basasa a Siriya.

https://p.dw.com/p/15YSn
ITAR-TASS: MOSCOW, RUSSIA. APRIL 10, 2012. Russia_s Foreign Minister Sergei Lavrov pictured during a joint press conference with his Syrian counterpart Walid Muallem. (Photo ITAR-TASS / Sergei Fadeichev), (c) picture alliance / dpa
Der russische Außenminister Sergei LawrowHoto: picture-alliance/dpa

A taƙaddamar da ake yi dangane da hanyoyin magance rikicin Siriya, ƙasar Rasha ta soki lamirin ƙasashen yamma da kakkausar lafazi. Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya faɗa wa manema labarai a birnin Mosko kafin wata ganawa da wakilin ƙasashen duniya na musamman a kan rikicin Siriya, Kofi Annan, cewa wasu ƙasashen yamma na ƙoƙarin ganin an yi yaƙin basasa a Siriya, inda suka dage a kan takunkuman kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya. Ya ce rashin azanci ne a ce shugaba Bashar al-Assad ya sauka domin ɗaukacin al'ummar ƙasar suna goya masa baya. Lavrov ya yi watsi da zargin da ake wa ƙasarsa na taimaka wa shugaba Assad.

"Muna goyon bayan shirin zaman lafiya na Kofi Annan da ƙudurin babban taron birnin Geneva na ranar 30 ga watan Yuni, wanda ya tanadi kafa gwamnatin riƙon ƙwarya a Siriya wadda za ta samun wakilcin dukkan ɓangarorin dake rikici a ƙasar."

A kuma halin da ake ciki dakarun gwamnatin Siriya da na 'yan tawaye na ci-gaba da gwanza ƙazamin faɗa a babban birnin ƙasar, Damaskus.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdullahi Tanko Bala