1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Rasha ta kori 'yan jaridar Jamus a kasarta

November 28, 2024

Fadar Kremlin da ke Moscow ta sanar da korar 'yan jaridar Jamus guda biyu wadanda ke gudanar da aikinsu a Rasha, matakin na zuwa a matsayin martani kan korar da hukumomin Berlin suka yiwa 'yan jaridar Rasha a Jamus.

https://p.dw.com/p/4nVac
Daliban da ke sanin makamar aikin jarida a hedikwatar DW a birnin Berlin
Daliban da ke sanin makamar aikin jarida a hedikwatar DW a birnin BerlinHoto: Stephanie Englert/DW

Sallamar 'yan jaridar na daga cikin takaddama da kuma takun-saka da ake samu tsakanin manema labarai da hukumomin Rasha. Ko a lokacin da Rasha ta kaddamar da farmaki kan Ukraine a watan Fabrairun 2022, hukumomin Rasha sun rufe babban ofishin yada labaran Deutsche Welle da ke birnin Moscow.

Karin bayani: An kori jami'in diflomasiyyan Birtaniya daga Rasha

Hukumomin kafar yada labaran Jamus ta ARD sun sanar da cewa wakilinsu da ke gudanar da aiki a kasar ta Rasha sun tabbatar musu da cewa an basu wa'adin daga nan zuwa tsakiyar watan Disambar 2024, dasu tattara yanasu-yanasu su fice daga kasar.