Rasha ta kori jami'an diplomasiyyar Jamus
April 22, 2023Talla
Wannan matakin na zuwa ne bayan da Rasha ta sha alwashin mayar wa Berlin da martani mai zafi a game da matakin da ta dauka na korar jami'an diflomassiyarta, fadar Kremlin ta ce korar jami'anta ba zai taba yin wani tasiri ba illa ya kara dagula lamura a dangantakarsu.
Kyakyawar dangantakar da ke a tsakanin kasashen biyu ta soma tsami, tun bayan da Rashan ta soma mamayar Ukraine a bara, kuma kasancewar Jamus a sahun gaban kasashen yamma da ke goyon bayan Ukraine, lamarin ya shafi huldarsu ta fuskar kasuwanci musanman kan batun makamashin gas.