Sojojin Ukraine a matsayin fursunonin yaki
May 20, 2022Talla
Sama da sojojin kasar Ukraine 1700 da suka mika wuya ga sojojin Rasha a ma'aikatar sarrafa karafa da ke birnin Mariupol ne Rashar ta ce ta na tsare da su a matsayin fursunonin yaki.
To sai dai Shugaba Volodmyr Zelensky na Ukraine, ya sha alwashin yin duk mai yiwuwa na kubutar da dadakarun sojin kasarsa. Zelensky ya ce zai yi amfani da abokan huldarsu da ke da karfin fada a ji na ganin Rasha ta gaggauta sako su.
Yawancin sojojin dai rahotanni na nuni da cewar tuni aka kai su yankin 'yan awaren kasar da ke samun goyon bayan Rashar.
Kungiyar kare hakkin bil'Adama ta amnesty international ta yi kira ga mahukuntan na Moscow da dole su mutunta yarjejeniyar kare fursunonin yaki, wacce ba ta aminta da ko kwarzane a kansu ba.