1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta kai hari Kherson

June 11, 2023

A kalla mutum uku ne suka mutu yayin da wasu 10 suka jikkata sakamakon harin da dakarun Rasha suka kai wa wani kwale-kwale a birnin Kherson da ke karkashin ikon Ukraine.

https://p.dw.com/p/4SRyR
Mutanen da ake kwashewa daga birnin Kherson sakamakon ambaliyar ruwa
Hoto: GENYA SAVILOV/AFP/Getty Images

Rahotanni sun yi nuni da cewa kwale-kwale na dauke da mutanen da ake ci gaba da kwashe wa daga birnin Kherson. Gwamnan yankin ya ce an kwashe mutanen ne sakamakon iftila'in ambaliyar ruwa da ta  auku a yankin, sanadiyyar tarwatsa madatsar Nova Kakhovka da gwamnatocin Kyiv da kuma Moscow ke zargin juna da aikatawa.

A cikin sanarwar da ya fitar, gwamnan ya ce daga cikin wadanda suka mutu har da wani dattijo mai shekaru 74 da ya sadaukar da rayuwarsa wajen tarewa wata mata harin da Rasha ta kai. Sai dai kuma bai bayyana ta yadda dakarun na Rasha suka kai harin ba. Rasha dai ta musanta zargin da ake mata na kaddamar da hare-hare kan fararen hula.