1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta kai hari babban birnin Ukraine, Kyiv

August 11, 2024

Rasha ta kai hare-haren jirage marasa matuka zuwa wasu yankunan Ukraine ciki har da babban birnin kasar, Kyiv.

https://p.dw.com/p/4jLIK
Hoto: Ilya Pitalev/Sputnik/IMAGO

Wani magidanci da dansa sun rasa rayukansu yayin da wasu mutum uku suka ji mummunan rauni, a hare-haren cikin dare da Rasha ta kai zuwa wasu yankunan Ukraine ciki har da babban birnin kasar Kyiv. Harin dai na zuwa ne yayin da ake fargabar kan cewa Moscow za ta mayar da martani kan harin da Ukraine ta kai mata a yankin Kursk.

Karin bayani: Rasha ta kai sabbin hare hare wajen Kyiv

Mukaddashin gwamnan yankin Kursk, ya yi kira ga hukumomi da su hanzarta kwashe fararen hula daga yankunan da ke da hatsari, yayin da Ukraine ta fadada kai hare-hare zuwa Rasha. Kafafen yada labaran Rasha sun ruwaito cewa, an kwashe fiye da mutane dubu 76 daga yankin tun bayan da Ukraine ta kai samamen ba zata zuwa yankin.