1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta ci gaba da kai hari duk da ikrarin janyewa

Suleiman Babayo
March 30, 2022

Dakarun Rasha sun ci gaba da kai farmaki wasu yankunan na arewacin Ukraine, tuni mahukuntan Ukraine din da na manyan kasashen yammacin duniya suka yi watsi da ikirarin Rasha na fara janyewa. 

https://p.dw.com/p/49FkY
Gine gine da aka lalata a yankin Chernihiv
Hoto: privat

Garin Chernihiv na arewacin Ukraine ya kwashe kwana guda cikin luguden wuta daga dakarun Rasha, inda fiye da mutane 100,000 da ke cikin birnin suka shiga tsaka mai wuya kan abinci da magunguna. Viacheslav Chaus ke zama gwamnan lardin ya yi karin haske kan abin da ya faru:

"A jiya Rasha ta fito fili ta ce ta rage dakaru a yankunan Chernihiv da Kiev. Za mu yarda da haka? Ina? ko kusa. Muna shirye da duk wani yanayi da za mu fuskanci abokan gaba a Chernihiv, wannan shi ne abin da muke yi. Ikirarin rage harkoki a Cheenihiv, ya fito fili da ruwan bama-bamai da makiya ke ci gaba da yi. Sun lalata gine-gine fararen hula, da wuraren karatu da shagunan kayayyaki, da gidaje masu yawa a Chernihiv"

Lalata gine gine a Chernihiv na kasar Ukraine
Lalata gine gine a Chernihiv na kasar UkraineHoto: privat

Haka na zuwa bayan bangarorin na Rasha da Ukraine sun gana a kasra Turkiyya bisa wani sabon shirin na neman kawo karshen kutsen da RAsha ta kaddamar a kan Ukraine. Kuma Dmytro Kuleba ministan harkokin wajen Ukraine ya jaddada matasayin kasar yayin zaman tattaunawar yana mai cewa "Ba za mu mika rayuwarmu da 'yancin kasarmu ba."

A daya bangaren mai magana da yawun fadar mulkin gwamnatin Kremlin ta Rasha Dmitry Peskov ya yaba da irin muradun da kasar Ukraine ta gabatar yayin tattaunawa a birnin Santanbul na Turkiyya, amma ya yi watsi da yiwuwar sake duba matsayin yankin Kiriya wanda ya ce ya koma karkashin ikon Rasha kuma karkashin tsarin mulkin kasar ta Rasha babu wanda yake da ikon tattauna makomar wani yanki na kasar.

Makamai da aka lalata a yaki tsakanin Rasha da Ukraine
Makamai da aka lalata a yaki tsakanin Rasha da UkraineHoto: Ichnyanske

Dominic Raab mataimakin firamnistan Birtaniya ya ce abin da ya saka kasashe duniya ke dari-dari saboda kasar Rasha ta saba yin baki biyu:

"Ba ma tunani mai yawa. Muna yanke hukuncin abin da Rasha ta fada da abin da ta aikata, ba abin da ta fada ba. Muna nuna dari-dari kan dagewa kan harkokin diflomasiyya. Haka yake cewa ko yaushe kokafofin diflomasiyya suna bude. Amma ban yi tsammani akwai wanda zai yarda da Putin ba game da yakin."

Shi dai Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya ba da umurnin kutse a kan Ukraine. A baya dakarun na Rasha sun yi yunkurin kewaye manyan garuruwan Ukraine da suka yi yunkurin kutsawa amma lamarin ya ci tura, kuma akwai rahotonnin da ke nuna cewa sojojin Ukraine suna kara samun nasarar tura dakarun na Rasha zuwa baya. A nasa bangaren Shugaba Volodymyr Zelenskiy na Ukraine ya bukaci kasashen Turai su kara bai wa kasarsa makamai da kuma kara takura Rasha kan matsi tattalin arziki har zuwa lokacin da mahukuntan na Rasha za su mika wuya kan yakin da suka kaddamar.