1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta ce hatsari ne canjin gwamnati a Siriya

June 6, 2012

Rasha ta yi gargaɗin cewar ci gaba da goyon bayan 'yan adawar Siriya ne ke janyo cikas ga yunƙurin warware rkicin ƙasar.

https://p.dw.com/p/158ug
epa03249669 Chinese President Hu Jintao (R) and Russian President Vladimir Putin (C) walk together after they reviewed an honor guard during a welcoming ceremony for the Shanghai Cooperation Organization (SCO) summit at the Great Hall of the People in Beijing, China, 05 June 2012. Russian President Vladimir Putin arrived in Beijing for talks that were expected to focus on Syria, bilateral energy cooperation, and other international issues. EPA/MARK RALSTON / POOL +++(c) dpa - Bildfunk+++
Shugaba Jintao na China da Putin na RashaHoto: picture-alliance/dpa

Ministan kula da harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, ya faɗi bayan wata ganawar da ta gudana a tsakanin shugaban Rasha Vladmir Putin da kuma magabatan ƙasar China a birnin Beijing cewar amincewa da buƙatar 'yan adawar Siriya na sauyin gwamnati a ƙasar, zai jefa yankin cikin mummunar matsala. Ministan ya ce a kullu-yaumin wasu ƙungiyoyin 'yan adawa daga wajen Siriya na ta kiraye-kirayen ƙaddamar da harin bam da zai kawo ƙarshen gwamnatin Assad, abinda kuma ya kwatanta da cewar yana da hatsarin gaske, kuma share fagen tsunduma yankin ne cikin mummunan yanayi. Ya ce kamata yayi a san cewar akwai ƙungiyoyi daban daban a Siriya waɗanda kuma ba za'a taɓa daidaita tsakanin su ba domin cimma matsaya guda.

Lavrov ya ce Rasha da China na bada cikakken goyon bayan su ga shirin warware rikicin Siriyar da Kofi Annan - mai shiga tsakani na ƙasa da ƙasa ya tsara, kuma ba za su lamunci matsayin 'yan adawar Siriya na gazawar shirin ba. Akan hakane ya buƙaci ƙasashen dake goyon bayan 'yan adawar dasu shawo kansu wajen mutunta shirin domin kawo ƙarshen rikicin da kuma fara tattaunawar sulhu. A halin da ake ciki kuma jakadan Jamus a Majalisar Ɗinkin Duniya Wittig Peter ya jaddada buƙatar shawo kan rikicin Siriya ta hanyar siyasa:

" Ya ce ina ganin dole ne muyi anfani da hanyoyin siyasa daban daban domin warware matsalar Siriya. Ban ga wani zaɓin daya fi hakan ba a yanzu, wanda zai kai ga shawo kan matsalar cikin ruwan sanyi, kuma ina zaton ɗaukar matakin soji ba shi ne ya dace ba.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu