1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Rasha ta ce Chadi ta kama 'yan kasarta uku ba dalili

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim MAB
September 24, 2024

Daga cikin wadanda kama akwai Shugaley, wanda EU ta sa wa takunkumi sakamakon aiki da jami'an Wagner karkashin Prigozhin

https://p.dw.com/p/4l1yC
Hoto: Russian Foreign Ministry/Handout via REUTERS

Rasha ta tabbatar da cewa gwamnatin Chadi ta kama 'yan kasarta uku da kuma wani 'dan kasar Belarus guda daya, ba tare bayyana wani dalilin kamen na su ba.

Karin bayani:Chadi: Cin hanci da karbar rashawa na karuwa a mulkin Deby

Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta bayyana sunayen 'yan kasarta da aka kama da Maxim Shugaley da Samer Sueifan, da kuma E. Tsaryov, da kuma 'dan Belarus mai suna A. Denisevich, to amma ta yi nisa wajen tattaunawa da gwamnatin Chadi domin sakin mutanen.

Karin bayani:Ministan harkokin wajen Rasha na ziyara a Afirka

Daya daga cikin wadanda kama mai suna Maxim Shugaley, na daga cikin mutanen da EU ta kakaba wa takunkumi, kasancewarsa guda cikin jigajigan jami'an da suka yi aiki da kamfanin tsaro na Wagner, karkashin jagorancin Yevgeny Prigozhin.