1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha na ƙara himma wajen samun haɗin kan Kirimiya

March 7, 2014

Tun bayan da majalisar dokokin Kirimiya ta dawo da zaɓen raba gardamarta baya zuwa 16 ga watan Maris, Rasha ke alƙawarin kyautatawa yankin idan ya haɗe da ita

https://p.dw.com/p/1BM1T
Vladimir Putin Duma
Vladimir Putin a gaban wakilan DumaHoto: picture-alliance/dpa

Yankin Kirimiya zai kasance sabon mamba a Tarayyar Rasha idan har mafi yawan 'yan asaslin yankin suka goyi bayan ɓallewa daga Ukraine, bayan ƙuri'ar raba gardamar da za a yi a ranar 16 ga watna Maris Idan Allah ya kai mu.

Kakakin majalisar dokokin Rasha Valentina Matvienko wadda ta gana da majalisar dokokin Kirimiyar yau ta ce wannan ya zo daidai da tsarin ƙasa da ƙasa, har ma ta kwatanta shi da ƙuri'ar jin ra'ayin da Scotland za ta yi na samun 'yancin kai daga Birtaniya a watan Satumba

To sai dai a yayin da Amirka ke tsaurara matakan samun takardun shiga ƙasarta wa Rashawa da 'yan asalin yankin na Kirimiya, bisa zarginsu da haddasa rashin daidaito a Ukraine, Shugabanin Ƙungiyar Tarayyar Turai sun dakatar da tattaunawar da suke yi kan sabbin hanyoyin haɗin gwiwa da sassauta dokokin shiga da fita tsakanin ƙasashen su.

Ko da shi ke firaministan Birtaniya David cameron ya ce daidaita lamuran a ƙasar Ukraine yanzu yana da mahimmanci sosai saboda nahiyar ta ɗauki tsawon lokaci ta tabbatar da cewa al'mmomin sun kai matsayin da suke a yanzu:

"Yana da mahimmanci saboda tarihi ya nuna mana cewa kawar da ido a lokutan da aka take haƙƙin al'ummomi, aka kuma ƙwace 'yancin kan da suke da shi, kan janyo ɗimbin matsaloli "

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe