1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin amfani da guba a yakin Ukraine

Binta Aliyu Zurmi
March 11, 2022

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai yi zaman gaggawa a zargin amfani da makamai masu guba a yakin da Rasha ke yi da Ukraine. A yayin da ake ci gab da gwabza fada a Ukraine.

https://p.dw.com/p/48KXR
Bildkombo | Wladimir Putin und Wolodymyr Selenskyj
Hoto: A. Gorshkov/SPUTNIK/AFP/Getty Images/Presidency of Ukraine/AA/picture alliance

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai yi wani zama na gaggawa a wannan Juma'ar domin tattauna bukatar Rasha da ke zargin kasar Ukraine na hada makamai masu yada kwayoyin cuta da taimakon Amirka.

Mahukuntan na Kremlin sun ce Amirka ce ta dauki nauyin binciken da aka yi na hada makaman da ke dauke da guba da suka ce ya yi wa wasu daga cikin sojojinsu illa.

Wannan zargi dai tuni Washington da Kyiv suka yi watsi da shi, inda suka ce alamoni sun nuna cewar Rashar ce ake zargin da tana gab da fara amfani da makaman da ke da guba a sabili da tirjiyar da take ci gaba da fuskanta.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Moscow ke zargin Amirka da amfanin da makaman da ke da guba ba, ta yi hakan a yakin kasar Syria  zargin da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gaza tabbatarwa.