Rasha na yunkurin kare kudurin Majalisar Dinkin Duniya kan Siriya
February 1, 2012Rasha tana ci gaba da hana ruwa gudu a kokarin gabatar da wani kudiri da zai yi barazanar dora takunkumi kan gwamnatin Syria a Damascus, idan har bata gaggauta kawo karshen rashin imani da keta hakin yan Adam a kasar, tare da baiwa jama'a karin democradiya ba. Wannan mataki na Rasha ya sanya duk da zaman muhawara da kwamitin sulhu yayi, babu wani abu sabo da aka cimma a zauren. Gwamnati a Moscow tana tsoron cewar gabatar da irin wnanan kudiri yana iya baiwa kasashen yamma damar katsalandan da karfin soja a Syria, kamar dai irin yadda ya faru a kasar Libya. Bugu da kari kuma, Rashan tana tsoron cewar bayan kawar da Mubarak a Masar da Gaddafi a Libya, Bashar al-ASsad shi kadai ya rage mai abokantaka da ita a yankin gabas ta tsakiya Rasha din tana kuma da dangantakar ciniki mai karfi da Damascus sansanin ta na soja a garin Tartus na Syria.
Wannan matsayi na Rasha ya zama babban kuskure, saboda a yunkurin amfani da ikon ta na hawa kujerar naki a kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya, a matsayin wata hanya ta ci gaba da dan abin da ya rage mata na angizo a al'amuran duniya, tana keta sharudda da dokokin da suka shafi kare mutunci da hakkin yan Adam. Rashan, a wani salo irin na zamanin daular Soviet, tana ci gaba da goyon bayan dan mulkin kama karya dake da jinin jama'a a hannuwansa. Goyon bayan da Moscow ta taba baiwa Saddam Hussein a Irak, shine yanzu take baiwa Bashar al-Assad a Syria. Duk da haka, Rashan tana sane da cewar ba zata kasance mai shiga tsakani da neman sulhu na hakika a Syria ba, sai ta yi nesa da shugaba Bashar al-Assad a kwamitin sulhu. Idan har Rashan bata yi haka ba, duk wani mataki da zata dauka, zai zama kamar dai neman ci gaba da goyon baya ne ga dan amshin shatan ta a Damascus, wanda yake kara shiga halin matsin lamba ta fuskar soja a kasar sa. Tun a yanzu ma, rahotanni suka ce mayakan yan adawa sun isa kusa da birnin Damascus. Wasu rade-radin sun nuna cewar yanzu haka kashi arba'in ne cikin dari na al'ummar Syria suke goyon bayan shugaban nasu.
To sai dai Rasha ta maida kanta saniyar ware a kwamitin sulhu, sakamakon matakinta na hana gabatar da kudiri kan Syria. Ko da shike China har yanzu tana goyon bayan matsayin na Rasha, amma mahukunta a Peking sun nuna shirin su na daidaaitawa da sabbin masu mulki a duniyar Larabawa, musamman saboda bukatun su na makamashi daga yankin.
Gwamnatin Putin ya kamata ta gane wadanda suka nuna goyon bayan su ga kudirin kan Syria, wanda ba kasashen yamma kadai suke goyon bayan sa ba. Kasar Morocco ce ta gabatarwa kwamitin sulhu shi, kuma yana samun goyon baya daga dukkanin kasashen kungiyar hadin kan Larabawa, wadanda ma suka nemi Assad ya sauka daga shugabancin Syria, ya mika madafun iko tsakanin kwanaki 15 ga mataimakin sa. Wannan kungiya ta goyi bayan kudirin ne bayan kasa samun nasarar aikin tawagar yan kallo da ta tura zuwa kasar ta Syria.
Kudirin na kasashen Larabawa watakila shine dama ta karshe ta hana Syria tsunduma gaba daya cikikn yakin basasa. Idan har ya mika mulki, Assad yana iya fita daga kasar zuwa gudun hijira a ketare, kamar dai yadda shugaban Yemen yayi, ba tare da an yi amfani da karfi domin aiwatar da canji a tsarin shugabancin kasar ta Syria ba. Yan adawa ana iya shigar dasu a aiykan mulki, tare da kare yancin tsiraru a wannan kasa, yayin da kasashen Larabawa zasu dauki matsayi na masu neman sulhu tsakanin dukkanin al'ummar kasar ta Syria. To sai dai ga duka wadannan abubuwa Rasha tace Njet, taki: kamar dai kasar ta Syria zata zama zakaran gwajin dafi ne na karfi da angizon Rasha, bayan kawo karshen zamanin yakin cacar-baka.
Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Mohammad Nasiru Awal