1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

EU: Dabarun rage tasirin Rasha a Afirka

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 13, 2023

Shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce, akwai bukatar kungiyar ta EU ta samar da sababbin dabaru wajen huldarta da kasashen Afirka domin dakile tasirin Rasha a nahiyar.

https://p.dw.com/p/4WIb3
EU | Hukumar Tarayyar Turai | Ursula von der Leyen | Afirka | Tasiri | Rasha
Shugabar Hukumar Tarayyar Turan Ursula von der LeyenHoto: Jean-Francois Badias/AP Photo/picture alliance

Shugabar Hukumar Tarayyar Turan Ursula von der Leyen ta bayyana hakan ne yayin jawabin da ta gabatar a gban majalisar Tarayyar Turan, inda ta bayar da misali da yankin Sahel da ta ce shi ne mafi talauci kana wanda ke bunkasa a bangaren yawan al'umma. A cewarta yawaitar juyin mulki a yankin, zai sake damalmala al'amura na tsawon lokaci. von der Leyen ta nunar da cewa Rasha na yin tasiri da kuma cin moriyar rudun da ake fama da shi a yankin, tana mai cewa ya kamata kungiyar EU ta nuna hadin kai wajen ceton Afirka kamar yadda ta nuna a kan Ukraine.