1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

Mutuwar Prigozhin ta sa ana zargin Rasha

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 25, 2023

Fadar Kremlin ta sa kafa ta yi fatali da jita-jitar da ake yada wa kan cewa, ita ce ta bayar da umurnin kisan shugaban rundunar Wagner Yevgeny Prigozhin.

https://p.dw.com/p/4VaR8
Russland | Gedenkstätte nach dem mutmaßlichen Tod von Jewgeni Prigoschin in Sankt Petersburg
Hoto: Anton Vaganov/REUTERS

Yevgeny Prigozhin dai ya halaka ne a wani hadarin jirgin saman 'yan kasuwa, watanni kusan biyu bayan ya jagoranci wani yunkurin yin bore ga shugabannin rundunar sojojin Rasha. Yayin wani taron manema labarai da ya gudanar, mai magana da yawun Shugaba Vladmir Putin na Rashan Dmitry Peskov ya bayyana cewa ana yada jita-jita mai yawan gaske dangane da mutuwar fasinjojin da ke cikin jirgin da suka hadar da Prigozhin. Ya kara da cewa da ma tilas a yada wannan jita-jita da wata manufa a Kasashen Yamma, yana mai cewa duka karya ce zalla kawai.