1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Rikicin Rasha da Ukraine sun hau teburin sulhu

Mouhamadou Awal Balarabe AMA/ZMA
February 28, 2022

Tawagogin Rasha da Ukraine sun fara tattaunawa a kasar Belarus a daidai lokacin da aka shiga rana ta biyar a yaki tsakaninsu, lamarin da ya sa kimanin 'yan Ukraine rabin miliyan kaurace wa kasarsu.

https://p.dw.com/p/47kM5
Belarus Verhandlungen zwischen Russland und Ukraine in der Region Gomel
Hoto: Alexander Kryazhev/ITAR-TASS/imago images

Wannan tattaunawar ta farko tsakanin bangarorin da ke fada da juna, ta zo ne a daidai lokacin da dakarun Vladimir Putin na Rasha suke fuskantar turjiya mai karfi daga sojojin Ukraine. Sannan kuma takunkumin da ba a taba ganin irinsa ba da kasashen yammacin duniya suka kakaba wa Rasha ke yi mummunan tasiri ga tattalin arzikin kasar.

Shugaban tawagar Rasha kuma mai ba da shawara a Kremlin Vladimir Medinski ya nuna cewa yana son cimma yarjejeniya da Kiev wacce za ta gamsar da bangarorin biyu. 

A nata bangaren, gwamnati Ukraine da ministan tsaro Oleksiï Reznikov ke wakilta a tattaunawar, ta yi kira ga sojojin Rasha da su ajiye makamansu tare da janyewa daga kasar. Kuma ta yi kira ga Kungiyar Tarayyar Turai da ta gaggauta amincewa da bukatar Ukraine na zama mamba na EU. Sai dai shugaban Majalisar zartaswa ta Tarayyar Turai Charles Michel ya jaddada cewa, ana samu sabanin ra'ayoyi game da kasancewar Ukraine a cikin kungiyar.

Karin Bayani : Rudani bayan fara yakin Rasha da Ukraine

Amma kasashen Kungiyar Tarayyar Turai sun sanar da cimma yarjejeniyar samar da makamai ga sojojin Ukraine a kan kudi Euro miliyan 450 da man fetur na Yuro miliyan 50. Kantomar harkokin wajen na EU Joseph Borell ya ce za a samar da kudin ne daga wani asusun gwamnatocin suka kafa a baya, domin ceto Ukraine daga halin da ta samu kanta a ciki.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa sama da mutane 500,000 ne suka kaurace wa Ukraine domin samun mafaka a wasu kasashe makwabta, tun bayan kazamin harin da sojojin Rasha suka fara kaiwa a ranar Alhamis. Shugabar Hukumar Kare Hakkin bil'Adama ta Majalisar Dinkin Duniya Michelle Bachelet ta yi kira da a samar da jagoranci mai karfi a daidai lokacin da ake fama da rikicin Ukraine. 

Dama dai Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta yi Allah wadai da amfani da wasu bama-bamai a Ukraine da suka kashe fararen hula ciki har da wani yaro, tana mai cewa ya kamata a gudanar da bincike a matsayin "laifi na yaki". 
 

Sharhi kan matsayar Jamus a rikicin Ukraine

veraltet - BITTE AUSSCHLIEßLICH 48048656 verwenden!
Hoto: DW

Jawabin shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya nuna sabuwar alkibla a dangantakar Jamus da Rasha da kuma manufofinta na tsaro. Kuma lokaci ya yi na yin hakan, inji babbar editan DW Manuela Kasper-Claridge.

Manuela ta ce jawabin mai karfi ne shugaban gwamnati Olaf Scholz ya gabatar a gaban majalisar dokoki ta Bundestag. Jawabin da ke nuni da cewar lokaci yayi da za a kawo karshen shakkun kan daukar mataki da kuma mikewa tsaye don fara tafiyar zahiri a siyasance. Jamus za ta aikiwa Ukraine makamai ka zalika za ta kashe kudi masu dumbin yawa a bangaren tsaro. Wannan na zama sabon babi, kuma zahiri kamar yadda shugaban gwamnatin ya sha nanatawa.

Karin Bayani : Jamus: Matakin sauya manufofin yaki

Gwamnatin kawancen Jamus dai ta fito fili ta nuna matsayinta kan wannan tabargaza da Rasha take yi. Daga karshe dai ana iya cewar, yanzu sauran kasashen da ke kawancen tsaro ta NATO musamman kasashen Baltic, sun san inda suke tare da Jamus. Kasancewar akwai fargabar cewar Putin zai so tilasta mata daukar bangare a kan Ukraine. Scholz ya bayyana karara cewa Berlin ba za ta amince da hakan ba, kuma za ta yi tsayin daka a kan manufofin kungiyar tsaro ta NATO.

Wannan ya zo akan gaba, saboda tsawon lokaci kenan babu abun da Jamus ta ke yi face watangaririya da mahawara a siyasance. Sai dai kuma yana da kyau a san cewar, sasantawar Jamus da Rasha abu ne da ke da muhimmanci a tarihin gina siyasar kasar, kamar yadda shugaban gwamnati Scholz ya jaddada. Wannan sako ne mai karfi zuwa ga al'ummar Rasha, wadanda ana iya cewar sun yi hadin kai dangane da yakin da Putin ke yi a Ukraine. Gangamin adawar da ake a biranen Rashan na tabbatar da haka. 

Sai dai gudu ba hanzari ba, wannan sabon matsayi na Jamus zai zo da tsada, wata kila ma mai ciwo. Rundunar tsaron kasar na shirin karbar karin tsabar kudi Euro biliyan 100 a cikin wannan shekarar kadai. Wajibe ne a tsuke bakin aljihu ta wani bangaren.

 

Russland Präsident Putin versetzt Atomstreitkräfte in Alarmbereitschaft
Hoto: Sergei Guneyev/AFP

Rasha na shirin zama saniyar ware a fannin tattali da kasuwar duniya. Illarda za a gani a nan take sun hada da tashin farashin makamashi, cikas wajen sarrafa kaya da rushewar wani bangare na kasuwanci. To sai dai da alamun mahukuntan na Jamus sun ballo ruwa, kuma dole Jamusawa su kasance cikin shiri.
 
Dole ne gwamnati ta gaggauta nuna yadda ya kamata kasar ta tunkari wannan da kuma irin illar da zai biyo baya - da kuma hadin kan 'yan adawa. Abun da ake bukata yanzu shi ne hadin kai, amma ba tare da barin tattaunawa mai muhimman ba. 

Daidai ne a karshe Jamus ta goyi bayan rufe bankunan Rasha daga tsarin biyan kuɗi na duniya na SWIFT. Amma a nan ma akwai bukatar a fayyace sakamakon da zai biyo baya. Akwai yiwuwar tsayar daina kwararar makamashin iskar gas din Rasha zuwa Jamus, domin idan ba tare da SWIFT ba, ba za a iya biyan kundin gas din ba. Matakin ramu na da nashi sakamako. Takunkumin yakan dauki lokaci kafin fara aiki.

Ga al'umar Ukraine da suka yin tsayin daka don kare kasarsu daga Rasha dai, wannan sauyin matsayi na Jamus a siyasance ya musu dai. Yanzu suna da tabbacin cewar, Berlin za ta yi musu wani abu fiye da aika hular kwano ta sojoji dubu biyar. Wannan sako ne mai muhimmanci daga shugaban gwamnatin kawancen na Jamus. Yanzu ana iya cewar, an san matsayin kasar.