1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

EU : Corona da Rasha na kan gaba a taron koli

Abdoulaye Mamane Amadou
December 16, 2021

Shugabanni da gwamnatocin kasashe membobin Kungiyar Tarayyar Turai na taron koli a binrin Bruxelles na kasar Beljiam, da zummar tattuna batutuwan da ke addabar yankin.

https://p.dw.com/p/44NLN
EU I Ursula von der Leyen
Hoto: Julien Warnand/AP/picture alliance

Batun rashin cikakken tsari don tunkarar sabon nau'in annobar corona na "Omicron" da na jibge sojojin Rasha a iyakarta da Ukraine na kan gaba daga cikin muhimman btutuwan da hukumomin kasashen EU za su mayar da hankali akai.

Babban jami'in dioflomasiyar kungiyar Josep Borrell, ya bayyana cewa kasashen kungiyar EU na goyon bayan Ukraine kan rikicinta da gwamnatin Moscow, kana kuma duk wasu matakan da Rasha ke dauka da suka saba ka'ida ka iya fuksntar hukunci mai tsanani daga kasashen.

Ana sa ran shuwagabannin su kebe waje daya don cikakken nazari kan wasu jerin takunkuman da suke ganin ya dace su kakaba wa Rasha a gabanin fitowa fili su bayyana su.