1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha da China sun toshe ƙudirin Kwamitin Sulhu a kan Siriya

July 19, 2012

Hakan na zuwa a daidai lokacinda dakarun gwamnatin Siriya ke ƙoƙarin kawar da 'yan tawaye daga yankunan birnin Damascus.

https://p.dw.com/p/15bQ5
(From L-R) Portuguese ambassador to the United Nations Jose Filipe Moraes Cabral, Russian ambassador to the United Nations Vitaly Churkin and South African ambassador to the United Nations Baso Sangqu vote during a Security Council meeting at the United Nations in New York April 21, 2012. The U.N. Security Council unanimously adopted a resolution on Saturday that authorizes an initial deployment of up to 300 unarmed military observers to Syria for three months to monitor a fragile week-old ceasefire in a 13-month old conflict. REUTERS/Allison Joyce (UNITED STATES - Tags: POLITICS)
Hoto: Reuters

Ƙasashen Rasha da China sun toshe ƙudirin Kwamitin Sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya kan ƙasar Siriya. Yayin da dakarun gwamnatin Siriya suka matsa ƙaimin kawar da 'yan tawaye cikin yankunan Damascus babban birnin ƙasar, bayan harin ƙunar baƙin wake da ya kai ga mutuwan wasu manyan jami'an gwamnati.

Wannan ƙudiri da zai ƙaƙaba takunkumi ga gwamnatin shugaba Bashar al-Assad. Jakadan Faransa a majalisar Gerard Araud ya shaida wa Kwamitin Sulhun cewa daƙile ƙudirin, ya zama hana mai shiga tsakani na ƙasashen duniya Kofi Annan matsin lamba da ya buƙata wajen warware rikicin.

Rashin sanin wurin da shugaba Assad yake

Ya zuwa yanzu babu bayanan inda shugaban ƙasar ta Siriya Bashar al-Assad, matarsa da 'ya'yansa uku, suke tun bayan harin ranar Laraba da ya hallaka manyan jami'an gwamnati da suka haɗa da ministan tsaro da mataimakinsa, wanda siriki ne ga shugaba Assad. Jami'an gwamnatin sun ce har kawo yanzu Assad yana fadar shugaban ƙasa inda yake ci gaba da jan ragamar mulki, amma 'yan adawa da majiyoyin diplomasiya sun ce ya yi ƙaura zuwa garin Letakia mai tashar jiragen ruwa.

Yayin da faɗa a kewayen birnin Damascus ya shiga kwanaki na biyar, mutane suna ci gaba da gudu daga birnin, jagoran sa ido na Majalisar Ɗinkin Duniya, Janar Robert Mood ya yi kakkausar suka kan harin, inda ya bayyana cewa ƙasar ba ta kan hanyar samun zaman lafiya. Wannan daidai lokacin da faɗa ya ƙara ƙazancewa tsakanin dakarun gwamnati da mayaƙan 'yan tawaye a kewayen gine ginen gwamnati.

Syria's President Bashar al-Assad speaks to the new government in Damascus in this handout photo distributed by Syrian News Agency (SANA) June 26, 2012. Al-Assad issued a decree to form a new government on Saturday, shaking up many cabinet posts but keeping the heads of the interior, defence and foreign ministries, state television reported. REUTERS/SANA/Handout (SYRIA - Tags: POLITICS) FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS. THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. IT IS DISTRIBUTED, EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS
Hoto: REUTERS

Yayin da ƙananan makamai ke ci gaba da wargaza lamura cikin ƙasar ta Siriya, tun da fari kafin jefa ƙuri'ar, babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-moon, wanda ya ziyarci ƙasar China, ya bayyana mahimmacin goyon baya daga ƙasar, kan matakan da Kwamitin Sulhu ke neman ɗauka na daƙile cikin dake ci gaba da bazuwar rikicin dake awun gaba da rayuka:

Buƙatar ɗaukar tsauraran matakai

"China za ta taka mahimmiyar rawa, wannan yana cikin dalilan da suka saka nake nan, nayi ƙoƙarin tattauna haka da shugabannin China, Shugaba Hu Jintao da ministan harkokin waje da sauran jami'ai, Kwamitin Sulhu ya ɗauki wasu matakai, amma akwai tsananin buri mai yawa, na cewa Kwamitin Sulhu ya haɗa kai, domin ɗaukar matakin ba sani ba sabo, domin shawo kan zubar da jinin."

Ban Ki-moon ya ƙara da cewa tilas Kwamitin ya ɗauki matakin na bai daya da zaiyi aiki, domin kawo ƙarshen abunda ke faruwa. Amma babu alamu wannan ziyara ta Ban zuwa birnin Beijing za ta sauya matsayin ƙasar kan abunda ke faruwa.

In this picture taken on Monday, June 25, 2012, Syrian rebels hold their rifles as they run to cross a street during a clashes with the Syrian forces troops, at Saraqeb town, in the northern province of Idlib, Syria. A United Nations probe into the killing of more than 100 civilians in the Syrian area of Houla last month says forces loyal to the government "may have been responsible" for many of the deaths. (Foto:Fadi Zaidan/AP/dapd).
Hoto: AP

Harin ranar Laraba ya janyo wa Kwamitin Sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya tsaiko kan ƙudirin da yake neman ɗauka kan matakan shawo rikicin ƙasar ta Siriya, ƙudirin dake samun goyon bayan ƙasashen yammacin duniya, kuma yanzu dai Rasha da China sun toshe wannan ƙudiri, wanda ba shi ne karon farko da suka yi haka ba.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal