Rasha da China sun juya baya game da Siriya
August 31, 2012Ko da shi ke ƙasashen yammancin duniya sun sake yin barazana ɗaukan mataki soja kan gwamnatin Bashar Al Assad, amma dai babu wata sanarwa da taron ya cimma sakamakon cikas da ake samu daga ƙasashen China da Rasha waɗanda basu halarci taron ba. Ana hasashen cewar ƙasashen duniyar da dama, na iya kai ga ɗaukan matakin soji ba tare da MDD kamar yadda ya faru a Kosovo a shekarar 1999.
Sai dai kuma ana ta ɓangaren Turkiya ta yi kira ga kwamitin tsaro na MDD da ya girka wani sansani 'yan gudun hijira a Siriya wanda zai riƙa samun kariya domin daƙile yunƙurin yan ƙasar zuwa gudun hijira a waje.Ministan harkokin waje na Turkiyar da ya baiyana haka a gaban kwamitin, ya ce ƙasar sa na da matsalar gaske wajan karɓar yan gudun hijira na Siriya da ke kwarraro masu aka- akai. Sai dai kwamitin na MDD na yin ɗari ɗari da buƙatar.Su kuwa ƙasashen Ingila da Faransa sun ba da sanarwa ba da gudunmawa ta biliyoyin daloli domin aikin agaji a Siriya.
Mawallafi: Abdourahamane Hasane
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe