1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha da China sun hau kujerar na-ƙi akan hukunta Siriya

Zainab MohammedOctober 5, 2011

Komitin sulhun Majalisar Ɗunkin Duniya ya bukaci ɗaukar tsauraran matakai akan Siriya

https://p.dw.com/p/12lmd
Hoto: AP

Rasha da China sun haɗa kawunan wajen hawan kujerar naƙi, akan daftarin Turai a komitin sulhun Majalisar Ɗunkin Duniya, da ke bukatar ayi Allah wadan Siriya, tare da ɗaukatkakaba mata takunkumi idan bata tsayar da kaiwa masu gangamin adawa hari ba. Ƙudurin ya samu ƙuri'un amincewar ƙasashe tara, a yayin da huɗu suka ƙi bayyana. Rasha da China sun kaɗa ƙuru'un ƙin amincewa da ƙudurin, wadda Faransa ce ta gabatar tare da goyon bayan Britaniya, Jamus da Portugal. ƙasashen turai ɗin dai sun shirya wannan ƙuduri ne da ke da nufin barazana shugaba al-Assad, na tsayar da harin da ake kaiwa 'yan adawa cikin kwanaki 30, ko kuma a ɗauki tsaauraran matakai a kan gwamnatinsa.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Usman Shehu Usman