Rarrabuwar kawunan kasashen Musulmai kan Siriya
August 14, 2012Shugabannin kungiyar kasashen Musulmi ta duniya OIC na gudanar da wani taro yanzu haka a birnin Makkah na kasar Saudi Arabiya inda su ke tattaunawa game da makomar Siriya a cikin kungiyar.
Gabanin taron dai, ministotocin harkokin wajen kungiyar da ke da mambobi 50 da bakwai sun bada shawarar korar Siriya daga kungiyar.
Sarki Abdallah Bin Saud na kasar ta Saudiyya ne dai ya bada shawarar kiran taron a wani yunkuri da ake ganin na karfafa gwiwar 'yan tawayen Siriya ne, a yunkurin da su ke yi na ganin shugaba Bashar al-Assad ya yi adabo da karagar mulki.
To sai dai duk da kasarin mabobin kungiyar na goyon bayan wannan matsayin da Sarki Abdallah ya dauka, a bangare guda Iran wadda shugabanta Mahmud Ahmedinijad ke hallartar taron ba ta goyon bayan batun korar Siriyan daga kungiyar. Wannan ya nuna irin rarrabuwar kawuna tsakanin ma biya darikar Sunni da wadanda ke bin darikar Shi'a.
Kazalika Iran din ta nuna rashin amicewar da abin da ta kira kokarin mahukuntan Saudiyyan da na Qatar da kuma Turkiyya na rura wutar rikicin Siriya wanda ke cigaba da janyo asarar rayuka.
Mawallafi: Mahmud Yaya Azare
Edita: Usman Shehu Usman