Zaben Jamus: Rangadin ma'aikatan DW
February 12, 2025Batun bakin haure da 'yan gudun hijra da na tattalin arziki, na daga cikin manyan batutuwan da jam'iyyun siyasar Jamus ke fafata yakin neman zabensu a kai. Tawagar DW da ke rangadi a yankunan Jamus domin ganin yadda yakin neman zaben ke tafiya ta ya da zango a Birnin Magderburg na arewacin kasar, birnin da a bara ya fuskanci harin ta'addanci da ya halaka mutane da dama. Gari ne dai mai tazarar kilomita 170 daga yammacin Berlin a yankin arewaci, Magdeburg guda ne daga cikin manyan biranen Jamus masu dumbin tarihi duk da cewa al'ummarsa ba su wuce dubu 240 ba a shekarar 2023.
Karin Bayani: Jamus: Kuri'ar yankar kauna kan gwamantin Scholz
Daya daga cikin muhimman tarihin da wannan birni ke da shi, sun hada wata kafariyar mujami'a da aka kafa shekaru aru-aru da kuma kasuwanni sayar da kayayyaki. A guda daga irin wannan kasuwar ce ma wani mahari ya kafa nasa bakin tarihi a ranar 20 ga watan Disambar bara, a daidai lokacin da mutane ke tsaka da cin kasuwar Kirismetti. Maharin ya sabo mota ya kutso a guje cikin tsakiyar kasuwar, inda ya halaka mutane shida tare da jikkata wasu akalla 300. Wannan na ci gaba da tayar da hankalin al'ummar birnin, musamman ma wadanda suka rasa danginsu. Harin ya kasance guda daga cikin 'yar manuniya a batun makomar bakin haure da 'yan ci-rani, ganin cewa mutumin da ya aikata ta'asar dan asalin kasar Saudiyya ne.
Hakan ya kuma sauya akalar batun yakin neman zaben gabanin wa'adi na 'yan majalisar dokoki da aka rusa mako guda bayan harin. Amidou Traoré wani Bajamushe ne mai tsatso da kasar Cote d'ivoire da ya shafe shekaru fiye da 24 a yankin, ya bayyana cewa harin na matukar tasiri ga yakin neman zaben da ke wakana a yanzu. Mai shekaru fiye da 50 a duniya, Traoure ya ce zai kada wa kuri'arsa ga jam'iyyar SPD da kawancenta ya ruguje. Hukumomi a Jamus sun bayyan cewa, kaso fiye da 50 cikin 100 ne jimillar masu neman mafaka da suka karu a bara fiye da na shekara ta 2022 da suka kai dubu 115 a fadin kasar.
Karin Bayani: Zaben Jamus 2025: Elon Musk na fatan nasara ga AfD
Batun bakin haure da 'yan gudun hijira na daga cikin manyan batutuwan da 'yan takara ke ta kai ruwa rana a kai, musamman ma a tsakanin jam'iyyar CDU da dan takararta Fredrich Merz ya fito karara ya bayyana manufofinsa na kawo gyara ga batun bakin haure da 'yan gudun hijira. A yayin da shi kuwa Olaf Scholz na jam'iyyar SPD ke cewa, ba a nan gizo ke saka ba. Wannan ma dai ba wata makawa batu ne da zai taka rawa wajen sauya ra'ayin masu kada kuri'a da dama, a zaben da za a gudanar a ranar 23 ga wannan wata na Fabarairu.