1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin ranar masoya ta duniya

Issoufou Mamane SB/ATB
February 14, 2023

Matasa na bikin ranar masoya da ke zama 14 ga watan Febrairun kowace shekara ko kuma Saint-Valentin inda da dama daga ciki ke ba da kyautatuka ga masoyansu yayin ya wasu ke tafiya guraren shakata.

https://p.dw.com/p/4NPdS
USA New York | Valentinstag
Alamar soyayyaHoto: Tayfun Coskun/AA/picture alliance

A fadin duniya matasa suna ranar da aka kebe domin masoya inda masoyan ke yi wa juna kautattuka tare da raya daren .Lokacin da sauran yankunan kasar ta Jamhuriyar Nijer ke wannan biki haka batun yake a jihar Tahoua inda matasa da dama ke wannan bikin na masoya inda wasu daga ciki ke sayen wasu abubuwa kawatan masoya.

Babu shakka a makamancin wannan lokacin na bikin Saint-Valentin masu shaguna na samun bunkasar sana'o'in musamman masu shagunan kayan kawa. To saidai kuma a dai wani bangaren wasu daga cikin matasan na fahimtar bikin ne da wata manufa ta daban musamman ganin wasu na shiga mawuyacin hali domin samun abin da za su bayar da sunan soyayya.