1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tunawa da masu aikin jinkai a duniya

Gazali Abdou Tasawa SB)(LMJ
August 19, 2022

Ranar ma'aikatan jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya. Bikin na zuwa ne lokacin da kungiyoyin jinkai ke fuskantar karancin kudin aiki a yankin Sahel yayin da mutane a yankin mai fama da matsalar tsaro ke bukatar agaji.

https://p.dw.com/p/4FnF2
Taimakon kungiyar Red Cross a Habasha
Jinkai a HabashaHoto: Ethiopian Red Cross Society South Omo Branch

A Jamhuriyar Nijar kungiyoyin agaji sun bi sahun takwarorinsu na raya ranar ma'aikatan agaji ta duniya wacce Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar a shekara ta 2008 domin tunawa da jami'an agaji na Majalisar Dinkin Duniya da suka mutu a wani hari da aka kai a cibiyarsu da ke a birnin Bagadaza na Iraki. A jamhuriyar Nijar bikin na bana ya zo ne a daidai lokacin da matsalolin tsaro da na sauran bala'o'i suka jefa miliyoin jama'a a cikin yanayi na dogaro da kungiyoyin agaji domin rayuwa.

Karin Bayani:Za a yi nazarin halin tsaro a Nijar

Ma'aikatar kula da ayyukan jinkai ta kasa ta bayyana cewa yanzu haka akwai kungiyoyin agaji dubu uku da 600 daga cikin dubu biyu da 700 na cikin gida wadanda ke gudanar da aikin agaji da na jinkai a cikin kasar baki daya. Sai dai guda 148 ne kawai ke aiki kai tsaye tare da gwamnati. Bikin na bana ya zo ne lokacin da matsalolin tsaro da na sauyin yanayi suka jefa miliyoyin jama'a cikin yanayin rayuwa ta hanyar taimakon agaji daga kungiyoyi. Albarkacin wannan rana ministan agaji na kasa ya jinjina wa kungiyoyin da kuma tunatar da rawar da suke takawa a kasar.

Taimakon kungiyar Red Cross a Habasha
Jinkai a HabashaHoto: Ethiopian Red Cross Society South Omo Branch

Bikin ranar ma'aikatan jinkai ta duniya ta bana ta zo lokacin da Jamhuriyar Nijar da kasashen Sahel ke fuskantar matsaloli na tsaro, wadanda Mahamadou Hama na hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce na kawo masu cikas a cikin aikin.

Wata matsalar ta daban da kungiyoyin agajin suke fuskanta ita ce ta rashin samun wadatattun kudin shiga, matsalar da amma Malam Abdourahmane Alkassoum ya ce suna shirin tunkara a karkashin wani taron kasa da kasa da suka yi wa suna "Salon international de Solidarite au Sahel."

Taimakon kungiyar Red Cross a Afghanistan
Jinkai a AfghanistanHoto: SAHEL ARMAN/AFP/Getty Images

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta bayyana cewa a shekarar da ta gabata kungiyoyin agaji 148 da ke aiki kai tsaye da gwamnati sun samar da kudi miliyan dubu 107 na CFA. Amma kuma ta koka kan yadda daga cikin kungiyoyin agaji dubu uku da 600 da ke aiki a kasar, kaso 23 daga cikin 100 ne kawai ke mutunta umurnin doka na gabatar da rahoton aikinsu a kowace shekara.