1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar fara riga-kafin corona a Amrika

December 14, 2020

Amirka na shirye-shiryen yi wa miliyoyin 'yan kasar allurar riga-kafin cutar corona. Ana sa ran fara yi wa ma'aikatan lafiya riga-kafin da wadanda suka manyanta.

https://p.dw.com/p/3mgoy
USA I Donald Trump nach der Präsidentschaftswahl
Hoto: Susan Walsh/AP/picture alliance

Yayin da ake shirin fara allurar riga-kafin cutar corona a Amirka a yau Litinin, Shugaba Donald Trump ya ce ba ya daga cikin wadanda za su karbi wannan allurar, bayan wasu kafafen labarai sun ruwaito cewa shugaban zai karbe ta.

Shugaba Trump ya ce babu sunansa daga cikin jerin wadanda za a yi wa allurar a tashin farko, sai dai ana iya yi masa nan gaba a lokacin da ya dace.

Ana sa ran fara yi wa ma'aikatan lafiya riga-kafin da wadanda suka manyanta sai kuma wadanda cutar ke iya tagayyarawa sosai.

Tun A jiya Lahadi ne dai manyan motocin daukar kaya masu firiji sun fara fita damiliyoyin alluaran kamfanin Pfizer da BioNtech da aka gikre a Kalamazoo da ke jihar Michigan, zuwa sassan Amirkar. 

A halin da ake ci ki dai akwai sama da mutum dubu 300 da cutar ta corona ta yi sanadin su a Amirka, yayin da adaddin wadanda ta kama ya zarta mutum miliyan 16.

A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Shugaba ya yi wa Amirka da duniya baki daya fatan samun waraka daga wannan cuta ta COVID-19, da a yanzu ta kashe sama da mutum miliyan daya da dubu 600 a duniya.