1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kujerar Ramaphosa na ashirin kufcewa

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 1, 2022

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa na fuskantar kiraye-kirayen ya sauka daga kan karagar mulki, bayan da wani bincike na majalisar dokokin kasar ya ce ya karya dokokin yaki da cin-hanci da rashawa.

https://p.dw.com/p/4KLYJ
Afirka ta Kudu | Cyril Ramaphosa | Makoma
Cyril Ramaphosa na jiran makomarsaHoto: Justin Tallis/AFP/Getty Images

Rahotanni sun nunar da cewa batun karya dokokin cin-hancin, na da nasaba da gidan gona mallakar Shugaba Cyril Ramaphosa. Tun da fari dai tsohon shugaban hukumar leken asiri ta kasar Arthur Fraser ne ya bayyana cewa, Ramaphosa ya yi kokarin boye makudan kudin da aka gano a gonar tasa a shekara ta 2020. Koda yake tuni Ramaphosa ya bayyana cewa, kudin da aka sata dalar Amirka dubu 580 kacal ba miliyan hudu da Fraser  ya yi zargi ba.

Haka kuma Ramaphosa ya musanta zargin yana da hannu a satar kudin, inda ya ce ba shi da masaniya a kansu. Tuni dai 'ya'yan jam'iyyar adawa da ma wasu daga jam'iyyarsa African National Congress ANC mai mulki, suka shiga cikin masu kiransa da ya sauka. A na sa ran shugabannin jam'iyyar ANC mai mulkin, za su yi wata ganawar gaggawa kan makomar Shugaba Ramaphosa.