1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

Zaben Kwango: Za a fara rajistar 'yan takara

September 1, 2023

Hukumar zaben Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta tsayar da ranar tara ga watan Satumba a matsayin ranar fara tantance masu sha'awar tsayawa takarar shugabancin kasa.

https://p.dw.com/p/4VrdF
Za a fara rijistar 'yan takaran shugaban kasa a KwangoHoto: Hereward Holland/REUTERS

Wannan na tabbatar da kankamar shirye-shiryen manyan zabbukan kasar ta Kwango wadanda za a gudanar a ranar 20 ga watan Disamba mai zuwa domin ba wa masu zabe miliyan 44 damar sake zaben sabbin jagororin kasar.

Karin bayani: Zaben Kwango ya mamaye jaridun Jamus

To sai dai a daidai lokacin da ake tunkarar zaben, 'yan adawa na zargin shugaba mai ci Felix Tshisekedi wanda zai sake tsayawa takara don neman wani wa'adin mulki a karo na biyu da shirya zabe marar tsafta.

Karin bayani: Tsugune ba ta kare ba a zaben kwango

Abokan hamayar na Tschisekedi na ci gaba da kalubalantar dokar zaben da aka yi wa kwaskwarima, tare kuma da zargin kafa hukumar zabe ta jeka na yi ka, baya ga kura-kurai wajen rijista masu zabe.