Rahoton hukumar kare hakin bil adama ta Human Right Wacth akan Siriya
December 15, 2011Talla
Hukumar kare hakin bil adama ta Human Rights Wacth ta baiyana wani rahoton wanda a cikin sa ta ke zargin sojojin ƙasar Siriya da laifin aikata kisan gila akan farara fula.Hukumar wacce ta ce ta tattauna da sojojin gwamnatin Bashar Al Assad wanɗada suka arce suka canza sheƙa domin bin bayan sahun masu gudanar da zanga zangar ta ce sun shaidama ta yadda aka aikata kisan.
Wani sojojin gwamnatin ƙasar Siriyan da ya amsa tambayoyin hukumar ta kare hakin bil adama ya baiyana halin da ya samu kansa a ciki ''ya ce masu harbin ɗauki ɗaya ɗaya guda biyu ke bani umarnin kafin hawa kan gine gine inda da gana muke yin harbi kan masu zanga zanga.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman